Ubangiji ya ce wa Musa, “Ga shi, ni da kaina, ina zuwa a gare ka cikin duhun girgije, domin jama'a su ji sa'ad da nake magana da kai, domin su amince da kai tutur.” Musa kuwa ya mayar wa Ubangiji da amsar da jama'ar suka bayar.
Ta haka Ubangiji ya riƙa yin magana da Musa baki da baki, kamar yadda mutum yakan yi magana da amininsa. Sa'ad da Musa ya koma cikin zango kuma, baransa, Joshuwa, ɗan Num, saurayi, ba zai fita daga cikin alfarwar ba.
Za su kuwa faɗa wa mutanen wannan ƙasa, gama sun riga sun ji, kai, ya Ubangiji, kana cikin tsakiyar jama'ar nan wadda kake bayyana kanka gare ta fuska da fuska. Girgijenka kuma yana tsaye a kansu, kakan kuma yi musu jagora da al'amudin wuta.
“Ubangiji ya faɗa wa taron jama'arku waɗannan dokoki da murya mai ƙarfi ta tsakiyar wuta, da girgije, da duhu baƙi ƙirin. Ya rubuta su a bisa alluna biyu na dutse, ya ba ni, ba abin da ya ƙara.”