Musa kuwa ya ɗauki jinin ya watsa wa jama'ar. Sa'an nan ya ce, “Wannan shi ne jinin alkawarin da Ubangiji ya yi da ku, wanda yake cikin dokokin nan duka.”
Allah kuwa ya ce, “Ga shi, na yi alkawari, cewa a gaban dukan jama'a zan aikata al'ajabai irin waɗanda ba a taɓa aikatawa a duniya ba, ko cikin wata al'umma. Dukan mutanen da kuke zaune tare da su za su ga aikina, gama zan aikata abin bantsoro a cikinku.
Wato alkawarin da na yi da kakanninku a lokacin da na fito da su daga ƙasar Masar, daga cikin tanderun ƙarfe. Na faɗa musu su yi biyayya da maganata, su aikata dukan abin da na umarce su. Ta haka za su zama mutanena, ni kuma in zama Allahnsu.
Ba irin wanda na yi da kakanninsu ba, sa'ad da na fito da su daga ƙasar Masar, alkawarin da suka karya, ko da yake ni Ubangijinsu ne, ni Ubangiji na faɗa.
Waɗannan ne zantuttukan alkawari da Ubangiji ya umarci Musa ya faɗa wa Isra'ilawa a ƙasar Mowab, wato banda alkawarin da ya yi da su a bisa Dutsen Horeb.
Saboda haka, ku lura fa, kada ku manta da alkawarin da Ubangiji Allahnku ya yi da ku, don haka kada ku sassaƙa wa kanku wata siffar kowane irin kamanni wanda Ubangiji Allahnku ya hana ku.
Musa ya kirawo Isra'ilawa duka, ya ce musu, “Ya ku Isra'ilawa, ku ji dokoki da farillai waɗanda nake muku shelarsu a yau! Sai ku koye su, ku aikata su sosai.