Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 5:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Musa ya kirawo Isra'ilawa duka, ya ce musu, “Ya ku Isra'ilawa, ku ji dokoki da farillai waɗanda nake muku shelarsu a yau! Sai ku koye su, ku aikata su sosai.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Musa ya tattara dukan Isra’ila ya ce, Ku ji, ya Isra’ila, ƙa’idodi da dokokin da na furta a kunnuwanku a yau. Ku koye su, ku kuma tabbata kun bi su.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 5:1
17 Iomraidhean Croise  

Ta haka su ma za su dogara ga Allah, Ba za su manta da abin da ya yi ba, Amma a kullum za su riƙa biyayya da umarnansa.


Ya ce, “In za ku himmantu ku yi biyayya da ni, ni da nake Ubangiji Allahnku, sai ku aikata abin da yake daidai a gare ni, ku kuma kiyaye umarnaina da dokokina duka, to, ba zan sa muku cuce-cuce irin waɗanda na sa wa Masarawa ba, gama ni ne Ubangiji da nake warkar da ku.”


Ka koya musu dokokin da umarnan, ka nuna musu hanyar da ya kamata su yi.


Don haka, sai ku kiyaye, ku kuma aikata duk abin da suka gaya muku, amma banda aikinsu. Don suna faɗa ne, ba aikatawa.


Waɗannan su ne zantuttukan da Musa ya faɗa wa dukan Isra'ilawa a hayin Urdun cikin jejin Araba daura da Suf, tsakanin Faran, da Tofel, da Laban, da Hazerot, da Dizahab.


“Sai ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, ku kiyaye faɗarsa, da dokokinsa da farillansa, da umarnansa kullum.


“Waɗannan su ne dokoki da farillai da za ku lura ku aikata a ƙasar da Ubangiji Allah na kakanninku ya ba ku, ku mallaka dukan kwanakinku a duniya.


Kada ya rabu da littafin, amma ya riƙa karanta shi dukan kwanakinsa domin ya koyi tsoron Ubangiji Allahnsa ta wurin kiyaye dukan dokoki da umarnai,


“Amma idan ba za ku yi biyayya da Ubangiji Allahnku ba, ko kuwa ba ku lura kuka aikata umarnansa da dokokinsa waɗanda nake umartar da su yau ba, to, dukan waɗannan la'ana za su auko muku, su same ku.


“Yau, ga ku nan tsaye, dukanku a gaban Ubangiji Allahnku, shugabannin kabilanku, da dattawanku, da shugabannin sojojinku, da dukan mazajen Isra'ila,


Sai Musa ya kira dukan Isra'ilawa ya ce musu, “Ai, kun ga dukan abin da Ubangiji ya yi wa Fir'auna da barorinsa a dukan ƙasar Masar.


“Yanzu, ya Isra'ilawa, sai ku kiyaye dokoki da farillai da nake koya muku don ku rayu, ku shiga ku kuma mallaki ƙasar da Ubangiji Allah na kakanninku suke ba ku.


da dukan Araba a hayin gabashin Urdun, har zuwa tekun Araba a gindin gangaren Fisga.


“Ga shi, na koya muku dokoki da farillai, yadda Ubangiji Allah ya umarce ni, don ku kiyaye su a ƙasa wadda kuke shiga ku mallake ta.


Ubangiji Allahnmu ya yi alkawari da mu a Horeb.


Sai ku himmantu ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, da farillansa, da dokokinsa waɗanda ya umarce ku da su.


Kada wannan littafin dokoki ya rabu da bakinka, amma zai zama abin da za ka yi ta tunani a kansa dare da rana domin ka kiyaye, ka kuma aikata bisa ga dukan abin da aka rubuta a ciki, gama ta haka za ka yi albarka cikin hanyarka, ta haka kuma za ka yi nasara.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan