Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 4:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Ko kuwa, da akwai wata babbar al'umma wadda take da dokoki da farillai na adalci kamar waɗannan dokoki da na sa a gabanku yau?”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Wace al’umma ce mai girma haka wadda take da ƙa’idodi da dokoki masu adalci kamar waɗannan ƙunshin dokokin da nake sa a gabanku a yau?

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 4:8
18 Iomraidhean Croise  

Ka kuma sauka a bisa Dutsen Sinai, Ka yi magana da jama'arka a can, Ka ba su ka'idodin da suka dace, Da dokoki, da kyakkyawar koyarwa.


Ka'idodin da ka bayar kuwa dukansu masu kyau ne, Daidai ne kuwa.


Koyarwarka masu adalci ne har abada, Ka ba ni ganewa domin in rayu.


Cibiyar dokarka gaskiya ce, Dukan ka'idodinka na adalci tabbatattu ne.


Umarnanka duka, abin dogara ne, Mutane suna tsananta mini da ƙarairayi, Ka taimake ni!


Na koya cewa ba wani abu da yake cikakke, Amma umarninka ba shi da iyaka.


A gaskiya da adalci aka kafa mulkinka, Akwai ƙauna da aminci a dukan abin da kake yi.


Gajimare da duhu sun kewaye shi. A kan adalci da gaskiya ya kafa mulkinsa.


Ubangiji shi Allah ne da ya ƙosa ya yi ceto saboda gaskiyarsa, Saboda haka yana so a girmama koyarwarsa,


Ko da na rubuta mata dokokina sau da yawo, Za ta ɗauke su wani baƙon abu ne kawai.


Ai kuwa, akwai ƙwarai, ta kowace hanya. Da farko dai, Yahudawa su ne aka amince wa a game da zantuttukan Allah.


Shi kuwa zai ɗaukaka ku ku zama abin yabo, masu suna, masu daraja, fiye da dukan al'umman da ya yi. Za ku zama jama'a tsattsarka ta Ubangiji Allahnku kamar yadda ya faɗa.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan