Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 4:7 - Littafi Mai Tsarki

7 “Gama babu wata babbar al'umma wadda allahnta yake kusa da ita kamar yadda Ubangiji Allahnmu yake kusa da mu sa'ad da muka kira gare shi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Wace al’umma ce mai girma haka wadda allolinta take kusa da su yadda Ubangiji Allahnmu yake kusa da mu a duk sa’ad da muka yi addu’a gare shi?

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 4:7
20 Iomraidhean Croise  

Ba wata al'umma kuma a duniya wadda take kama da jama'arka Isra'ila, wadda kai Allah ka fansa ta zama jama'arka. Ka mai da kanka sananne. Ka yi wa jama'arka manyan abubuwa masu banmamaki. Ka kori al'ummai da gumakansu a gaban jama'arka, waɗanda ka fansa daga Masar.


Yana kusa da dukan waɗanda suke kira gare shi, Waɗanda suke kiransa da zuciya ɗaya.


Bai yi wa sauran al'umma wannan ba, Domin ba su san dokokinsa ba. Yabo ya tabbata ga Ubangiji!


Ya sa al'ummarsa ta yi ƙarfi, Domin dukan jama'arsa su yabe shi Jama'arsa Isra'ila, wadda yake ƙauna ƙwarai! Yabo ya tabbata ga Ubangiji!


Adalai sukan yi kira ga Ubangiji, yakan kuwa kasa kunne, Yakan cece su daga dukan wahalarsu.


Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai, Yakan ceci waɗanda suka fid da zuciya.


Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu, Kullum a shirye yake yă yi taimako a lokacin wahala.


Amma a gare ni, ya fi mini kyau, in kasance kusa da Allah! Na sami mafaka a wurin Ubangiji Allah, Da zan yi shelar dukan abin da ya aikata.


Hakika a shirye yake yă ceci waɗanda suke girmama shi, Kasancewarsa a ƙasar, ceto ne ga ƙasar.


Zan ba da dukan al'ummai don in ceci ranku, Gama kuna da daraja a gare ni, Gama na ba ku girma, ina kuma ƙaunarku.


Ku juyo wurin Ubangiji, ku yi addu'a gare shi, Yanzu da yake kusa.


Bai ga mugunta ga Yakubu ba, Bai kuma ga wahala a Isra'ilawa ba. Ubangiji Allahnsu yana tare da su, Suna sowar murna domin shi sarkinsu ne.


Gama daga kan duwatsu na gan su, Daga bisa kan tuddai na hange su, Jama'a ce wadda take zaune ita kaɗai, Sun sani sun sami albarka fiye da sauran al'ummai.


wato nufinsa shi ne su neme shi, ko watakila sā laluba su same shi, alhali kuwa ba ya nesa da kowane ɗayanmu.


Shi kuwa zai ɗaukaka ku ku zama abin yabo, masu suna, masu daraja, fiye da dukan al'umman da ya yi. Za ku zama jama'a tsattsarka ta Ubangiji Allahnku kamar yadda ya faɗa.”


Mai farin ciki ne kai, ya Isra'ila! Wane ne kamarku, mutanen da Ubangiji ya ceta? Ubangiji ne garkuwarku, Shi ne kuma takobinku mai daraja. Magabtanku za su yi muku fādanci, Amma ku za ku tattake masujadansu.”


“Ku tambaya mana, ko a kwanakin dā kafin zamaninku, tun ma daga lokacin da Allah ya yi mutum a duniya, ku tantambaya daga wannan kusurwa ta samaniya zuwa waccan, ko wani babban abu irin wannan ya taɓa faruwa, ko kuma an taɓa jin labarin irinsa?


Akwai wani ɗan adam wanda ya taɓa jin muryar Allah, Allah Mai Rai yana magana ta tsakiyar wuta yadda muka ji, har ya rayu?


Ku kusaci Allah, shi ma zai kusace ku. Ku tsarkake al'amuranku, ya ku masu zunubi. Ku kuma tsarkake zukattanku, ya ku masu zuciya biyu.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan