Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 4:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Ku kiyaye su, ku aikata su, gama yin haka zai tabbatar wa sauran al'ummai, kuna da hikima da ganewa. Sa'ad da al'ummai za su ji waɗannan dokoki, za su ce, ‘Ba shakka, wannan babbar al'umma tana da hikima da ganewa.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Ku kiyaye su, ku aikata su, gama yin haka zai tabbatar wa sauran al’ummai, kuna da hikima da ganewa. Sa’ad da al’ummai za su ji waɗannan dokoki, za su ce, “Ba shakka, wannan babbar al’umma tana da hikima da ganewa.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 4:6
27 Iomraidhean Croise  

Sarakuna daga ko'ina a duniya, sun ji labarin hikimarsa, suka kuma aika da mutane don su ji shi.


“Allah ya ce wa mutane, ‘Duba, tsoron Ubangiji shi ne hikima, Rabuwa da mugunta kuma, ita ce haziƙanci.’ ”


Hanyar samun hikima, ita ce tsoron Ubangiji, Yakan ba da kyakkyawar ganewa Ga dukan waɗanda suke bin umarnansa, Sai ku yabe shi har abada!


Dokar Ubangiji cikakkiya ce, Tana wartsakar da rai. Umarnan Ubangiji abin dogara ne, Sukan ba da hikima ga wanda ba shi da ita.


Ka'idodin Ubangiji daidai suke, Waɗanda suke biyayya da su sun ji daɗi. Umarnan Ubangiji daidai suke, Sukan ba da fahimi ga zuciya.


Sukan sa marar sani ya zama masani, sukan koya wa samari yadda za su zama masu amfani.


Waɗannan karin magana sukan ƙara wa masu ilimi hikima, sukan zama jagora ga masana,


In kana so ilimi dole ne ka fara da tsoron Ubangiji. Jahilai ba su san darajar hikima ba, sun kuwa ƙi su koya.


Adalci yakan ɗaukaka al'umma, amma zunubi yakan kunyatar da al'umma.


Me ya sa haziƙi yake da hikima? Domin ya san abin da zai yi. Me ya sa dakiki yake wauta? Domin yana ganin kansa masani ne.


Ubangiji shi Allah ne da ya ƙosa ya yi ceto saboda gaskiyarsa, Saboda haka yana so a girmama koyarwarsa,


Za a kunyatar da masu hikima. Za su tsorata, za a kuma tafi da su. Ga shi, sun ƙi maganar Ubangiji. Wace hikima suke da ita?


Ubangiji Allah ya ce, “Wannan ita ce Urushalima. Na kafa ta a tsakiyar al'ummai da ƙasashe kewaye da ita.


A cikin dukan abin da ya shafi hikima da ganewa wanda sarki ya nemi shawararsu, sai ya tarar sun fi dukan masu sihiri da bokaye waɗanda suke cikin mulkinsa har sau goma.


‘Ya Belteshazzar shugaban masu sihiri, tun da yake na san ruhun alloli tsarkaka yana a cikinka, ba wani asirin da zai fi ƙarfin ganewarka. Ga mafarkin da na yi, sai ka faɗa mini fassararsa.


Ko da na rubuta mata dokokina sau da yawo, Za ta ɗauke su wani baƙon abu ne kawai.


Sa'an nan jama'ar dukan al'ummai za su ce ku masu farin ciki ne, gama ƙasarku za ta yi daɗin zama.”


Saboda haka sai ku kiyaye, ku aikata dukan zantuttukan wannan alkawari don ku arzuta a cikin dukan abin da za ku yi.


ya ce musu, “Ku riƙe dukan waɗannan kalmomi a zuciyarku, waɗanda nake yi muku kashedi da su a yau don ku umarci 'ya'yanku su kiyaye dukan maganar dokokin nan sosai.


Wannan ba magana kurum ba ce, amma ranku ne. Ta wurin wannan magana ce za ku yi tsawon rai a ƙasar da za ku haye Urdun zuwa ciki don ku mallake ta.”


da kuma yadda tun kana ɗan ƙaramin yaro ka san Littattafai masu tsarki, waɗanda suke koya maka hanyar samun ceto ta dalilin bangaskiya ga Almasihu Yesu.


Ina mai hikima da fahimi a cikinku? To, ta kyakkyawan zamansa sai ya nuna aikinsa da halin tawali'u da hikima suke sawa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan