Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 4:5 - Littafi Mai Tsarki

5 “Ga shi, na koya muku dokoki da farillai, yadda Ubangiji Allah ya umarce ni, don ku kiyaye su a ƙasa wadda kuke shiga ku mallake ta.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Ga shi, na koya muku ƙa’idodi da dokoki, yadda Ubangiji Allahna ya umarce ni, don ku bi su a ƙasar da za ku shiga ku mallaki.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 4:5
24 Iomraidhean Croise  

Kai ne ka koya mini, ya Allah, tun lokacin da nake yaro, Har wa yau kuwa ina ba da labarin ayyukanka masu banmamaki.


Ka koya musu dokokin da umarnan, ka nuna musu hanyar da ya kamata su yi.


Ubangiji kuma ya ce mini, “Ka yi shelar dukan maganan nan a biranen Yahuza da titunan Urushalima duka, cewa su ji maganar alkawarin nan, su aikata.


Na ba su dokokina da ka'idodina, waɗanda idan mutum ya kiyaye su, zai rayu.


“Sai ku kiyaye dokokina. Kada ku bar dabbobinku su yi barbara da waɗansu iri dabam. Kada ku shuka iri biyu a gonakinku. Kada ku sa tufar da aka yi da ƙyalle iri biyu.


Waɗannan su ne dokoki, da ka'idodi, da umarnai waɗanda Ubangiji ya yi tsakaninsa da Isra'ilawa ta hannun Musa a bisa Dutsen Sinai.


Waɗannan su ne umarnan da Ubangiji ya ba Musa a kan Dutsen Sinai saboda isra'ilawa.


Waɗannan su ne umarnan da Ubangiji ya ba Musa a Dutsen Sina'i, can cikin hamada, a ranar da ya faɗa wa Isra'ilawa su kawo hadayunsu gare shi.


kuna koya musu su kiyaye duk iyakar abin da na umarce ku. Ga shi, ni kuma kullum ina tare da ku har zuwa matuƙar zamani.”


domin ban ji nauyin sanar da ku dukan nufin Allah ba.


Sai dai kowa ya auna kansa, sa'an nan ya ci gurasar, ya kuma sha a ƙoƙon.


Jawabi mafi muhimmanci da na sanar da ku, shi ne wanda na karɓo, cewa, Almasihu ya mutu domin zunubanmu, kamar yadda Littattafai suka faɗa,


sai ku lura, ku aikata dukan dokoki da farillai waɗanda nake sawa a gabanku yau.”


“Yanzu, ya Isra'ilawa, sai ku kiyaye dokoki da farillai da nake koya muku don ku rayu, ku shiga ku kuma mallaki ƙasar da Ubangiji Allah na kakanninku suke ba ku.


Kada ku ƙara, ko ku rage kome daga cikin abin da na umarce ku, amma ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, waɗanda nake umartarku da su.


Amma ku da kuka dogara ga Ubangiji Allahnku, a raye kuke har yau.


Sai ku kiyaye dokokinsa da umarnansa waɗanda na umarce ku da su yau, don zaman lafiyarku da na 'ya'yanku a bayanku, domin kuma ku yi tsawon rai a ƙasa wadda Ubangiji Allahnku yake ba ku har abada.”


Musa ya kirawo Isra'ilawa duka, ya ce musu, “Ya ku Isra'ilawa, ku ji dokoki da farillai waɗanda nake muku shelarsu a yau! Sai ku koye su, ku aikata su sosai.


“Waɗannan su ne umarnai, da dokoki, da farillai waɗanda Ubangiji Allahnku ya umarce ni in koya muku domin ku kiyaye su a ƙasar da kuke hayewa zuwa ciki don ku mallake ta,


Saboda haka, sai ku kiyaye umarnai, da dokoki, da farillai ku aikata su, wato waɗanda nake umartarku da su yau.”


“Ku kula fa, don kada ku manta da Ubangiji Allahnku, ku ƙi kiyaye umarnansa, da farillansa, da dokokinsa waɗanda na umarce ku da su yau.


To, shi Musa mai aminci ne ga dukkan jama'ar Allah a kan shi bara ne, saboda shaida a kan al'amuran da za a yi maganarsu a nan gaba,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan