Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 4:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Kada ku ƙara, ko ku rage kome daga cikin abin da na umarce ku, amma ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, waɗanda nake umartarku da su.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Kada ku ƙara, kada ku rage daga cikin abin da nake umarce ku. Amma ku kiyaye umarnan nan na Ubangiji Allahnku, da na ba ku.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 4:2
21 Iomraidhean Croise  

Ta haka su ma za su dogara ga Allah, Ba za su manta da abin da ya yi ba, Amma a kullum za su riƙa biyayya da umarnansa.


Kada ka yi ƙari a kan maganarsa, don kada ya tsauta maka, a kuma bayyana kai maƙaryaci ne.”


Bayan wannan duka, makasudin maganar shi ne, ka yi tsoron Allah, ka kiyaye dokokinsa, gama wannan shi ne wajibi ga mutum.


“Ka tsaya a filin Haikalin Ubangiji, ka yi wa dukan biranen Yahuza magana, su waɗanda suka zo Haikalin Ubangiji domin su yi sujada. Ka faɗa musu dukan maganar da na umarce ka, kada ka rage ko ɗaya.


Hakika ina gaya muku, kafin sararin sama da ƙasa su shuɗe, ko wasali ko ɗigo na Attaura ba za su shuɗe ba, sai an cika dukan kome.


“Kun dai ji an faɗa, ‘Ka so ɗan'uwanka, ka ƙi magabcinka.’


To, 'yan'uwa, bari in yi muku misali. Ko alkawari na mutum ne kawai, in dai an riga an tabbatar da shi, ba mai soke shi, ba kuma mai ƙara wani abu a kai.


A shekara ta arba'in, a rana ta fari ga watan goma sha ɗaya, Musa ya faɗa wa Isra'ilawa dukan abin da Ubangiji ya umarce shi ya faɗa musu.


“Ku lura, ku aikata dukan abin da na umarce ku da shi, kada ku ƙara, kada ku rage daga cikinsa.


“Idan wani annabi, ko mai mafarki ya fito a cikinku, ya yi muku shelar wata alama ko mu'ujiza,


Musa ya ba mu dokoki, Abin gādo ga taron jama'ar Yakubu.


Duk da haka Ubangiji ya umarce ni in koya muku dokokin da farillan don ku aikata su a ƙasar da kuke hayewa zuwa ciki don ku mallake ta.”


Sai ku kiyaye dokokinsa da umarnansa waɗanda na umarce ku da su yau, don zaman lafiyarku da na 'ya'yanku a bayanku, domin kuma ku yi tsawon rai a ƙasa wadda Ubangiji Allahnku yake ba ku har abada.”


“Ga shi, na koya muku dokoki da farillai, yadda Ubangiji Allah ya umarce ni, don ku kiyaye su a ƙasa wadda kuke shiga ku mallake ta.


Da ma kullum suna da irin wannan zuciya ta tsorona, da za su kiyaye dukan umarnaina, zai zama fa'ida gare su da 'ya'yansu har abada.


“Sai ku lura ku yi daidai bisa ga abin da Ubangiji Allahnku ya umarce ku, kada ku kauce dama ko hagu.


Ka dai dāge, ka yi ƙarfin hali ƙwarai, kana kiyaye dukan dokokin da bawana Musa ya umarce ka da su. Kada ka kauce musu dama ko hagu, gama da haka nan za ka arzuta cikin dukan harkokinka.


Babu wata kalmar da Musa ya umarta, da Joshuwa bai karanta a gaban dukan taron Isra'ilawa ba, tare da mata da ƙanana, da baƙin da suke zaune tare da su.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan