Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 4:16 - Littafi Mai Tsarki

16 don kada ku yi mugunta, ku sassaƙa wa kanku wata siffar kowane abu, ko siffar mace ko ta namiji,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 don kada ku lalace, ku kuma yi wa kanku gunki, siffa ta wani kama, ko a kamannin namiji, ko kuwa ta mace,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 4:16
22 Iomraidhean Croise  

Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Sauka, gama jama'arka da ka fito da su daga ƙasar Masar sun ƙazantar da kansu.


Da wa za a iya kwatanta Allah? Wa zai iya faɗar yadda yake?


Masassaƙi yakan auna itace. Ya zana siffa da alli, sa'an nan ya sassaƙe shi da kayan aikinsa. Ya yi shi da siffar mutum kyakkyawa, domin a ajiye shi a masujadarsu.


Da na shiga, sai na ga zānen siffofin kowane irin abu mai rarrafe, da haramtattun dabbobi, da dukan gumakan mutanen Isra'ila kewaye da bangon.


“Kada ku juya ku bi gumaka, ko kuma ku yi wa kanku gumaka na zubi. Ni ne Ubangiji Allahnku.


Ubangiji ya ce, “Kada ku yi wa kanku gumaka, ko ku kafa sassaƙaƙƙiyar siffa, ko al'amudi. Kada kuma ku kafa wata siffa ta dutse a ƙasarku da za ku durƙusa mata, gama ni ne Ubangiji Allahnku.


Allah Ruhu ne, masu yi masa sujada kuwa lalle su yi masa sujada a ruhu, da gaskiya kuma.”


To, da yake mu zuriyar Allah ne, ai, bai kamata mu tsammaci Allah na kama da wata surar zinariya, ko ta azurfa, ko ta dutse ba, wadda mutum ya ƙago ta dabararsa.


Kada kuma ku kafa al'amudi, abin da Ubangiji Allahnku yake ƙi.”


“ ‘La'ananne ne mutumin da ya sassaƙa, ko ya ƙera gumaka, abar ƙyama ce ga Ubangiji, aikin hannun mai sana'a, ya kafa ta a ɓoye.’ “Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’


Gama na sani bayan rasuwata za ku aikata mugunta, ku kauce daga hanyar da na umarce ku. Masifa za ta auko muku a kwanaki masu zuwa saboda za ku aikata mugunta a gaban Ubangiji, za ku tsokani fushinsa da aikin hannuwanku.”


Saboda haka, ku lura fa, kada ku manta da alkawarin da Ubangiji Allahnku ya yi da ku, don haka kada ku sassaƙa wa kanku wata siffar kowane irin kamanni wanda Ubangiji Allahnku ya hana ku.


“Sa'ad da kuka haifi 'ya'ya, kuka sami jikoki, kuka kuma daɗe cikin ƙasar, idan kuka yi abin da yake haram, wato kuka yi gunki na sassaƙa na kowace irin siffa, kuka kuma aikata mugunta a gaban Ubangiji Allahnku har kuka tsokane shi ya yi fushi,


“ ‘Kada ka yi wa kanka gunki, ko wata siffar abin da yake a sama a bisa, ko siffar abin da yake a duniya a ƙasa, ko siffar abin da yake a cikin ruwa a ƙarƙashin ƙasa.


Kada ka yi musu sujada, ko ka bauta musu, gama ni Ubangiji Allahnka, Allah mai kishi ne, nakan hukunta 'ya'ya, da jikoki saboda laifin iyaye waɗanda suka ƙi ni.


“Sa'an nan ya ce mini, ‘Tashi, ka gangara da sauri, gama jama'arka wadda ka fito da ita daga Masar ta aikata mugunta, ta kauce da sauri daga hanyar da na umarce ta ta bi. Ta yi wa kanta gunki na zubi.’


Girma da ɗaukaka su tabbata ga Sarkin zamanai, marar mutuwa, marar ganuwa, Allah Makaɗaici, har abada abadin. Amin, amin.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan