Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 4:10 - Littafi Mai Tsarki

10 da yadda kuma a waccan rana kuka tsaya a gaban Ubangiji Allahnku a Horeb, sa'ad da Ubangiji ya ce mini, ‘Ka tattara mini jama'a domin su ji maganata, su koyi tsorona dukan kwanakinsu a duniya, su kuma koya wa 'ya'yansu.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Ku tuna da ranar da kuka tsaya a gaban Ubangiji Allahnku a Horeb, sa’ad da ya ce mini, “Ka tara mutane a gabana, don su ji maganata, su koya yin mini bangirma muddin ransu a ƙasar, su kuma iya koyar da su ga ’ya’yansu.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 4:10
25 Iomraidhean Croise  

Gama na zaɓe shi don ya umarci 'ya'yansa da gidansa domin su kiyaye tafarkin Ubangiji a bayansa, su riƙe adalci da shari'a.” Ubangiji ya tabbatar wa Ibrahim da abin da ya alkawarta masa.


Za a yabi abin da ka aikata daga tsara zuwa tsara, Za su yi shelar manya manyan ayyukanka.


Isra'ilawa sun kai jejin Sina'i a farkon watan uku bayan fitowarsu daga ƙasar Masar.


Su shirya saboda rana ta uku, gama a kan rana ta uku zan sauko a bisa dutsen Sina'i a gabansu duka.


A safiyar rana ta uku aka yi tsawa, da walƙiyoyi, da girgije mai duhu a bisa dutsen, aka tsananta busar ƙaho, sai dukan jama'ar da suke cikin zango suka yi rawar jiki.


Ubangiji ya ce wa Musa, “Ga shi, ni da kaina, ina zuwa a gare ka cikin duhun girgije, domin jama'a su ji sa'ad da nake magana da kai, domin su amince da kai tutur.” Musa kuwa ya mayar wa Ubangiji da amsar da jama'ar suka bayar.


Da jama'a suka ji tsawar hadiri, da ƙarar ƙaho mai tsanani suka kuma ga walƙiya, da dutsen yana hayaƙi, sai suka ji tsoro suka yi rawar jiki, suka tsaya nesa.


Musa kuwa ya ce wa jama'a, “Kada ku ji tsoro, gama Allah ya zo ne don ya jarraba ku, don ku riƙa girmama shi, don kuma kada ku yi zunubi.”


Bayan wannan duka, makasudin maganar shi ne, ka yi tsoron Allah, ka kiyaye dokokinsa, gama wannan shi ne wajibi ga mutum.


Masu rai ne suke yabonka, Kamar yadda nake yabonka yanzu. Iyaye za su faɗa wa 'ya'yansu irin amincinka.


Daga zamanai ya zuwa wani zamani, Jinƙansa yana ga waɗanda suke tsoronsa.


Za ku koya wa 'ya'yanku su, ku yi ta haddace su, sa'ad da kuke zaune a gida, da sa'ad da kuke tafiya, da sa'ad da kuke kwance, da sa'ad da kuka tashi.


“Waɗannan su ne dokoki da farillai da za ku lura ku aikata a ƙasar da Ubangiji Allah na kakanninku ya ba ku, ku mallaka dukan kwanakinku a duniya.


Ku ci zakar sabon hatsinku, da ruwan inabinku, da manku, da 'yan fari na shanunku, da tumakinku, a gaban Ubangiji Allahnku, a wurin da zai zaɓa ya tabbatar da sunansa, don ku koyi tsoron Ubangiji Allahnku har abada.


Kada ya rabu da littafin, amma ya riƙa karanta shi dukan kwanakinsa domin ya koyi tsoron Ubangiji Allahnsa ta wurin kiyaye dukan dokoki da umarnai,


“Sai ku lura, ku kiyaye kanku sosai, don kada ku manta da abubuwan da kuka gani da idonku kada kuma su fita a ranku dukan kwanakinku. Ku sanar wa 'ya'yanku da jikokinku da su,


Ubangiji Allahnmu ya yi alkawari da mu a Horeb.


Da ma kullum suna da irin wannan zuciya ta tsorona, da za su kiyaye dukan umarnaina, zai zama fa'ida gare su da 'ya'yansu har abada.


don ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku da 'ya'yanku da jikokinku, ku kuma kiyaye dukan dokokinsa da umarnansa, waɗanda nake umartarku dukan kwanakinku don ku yi tsawon rai.


Sai ku koya wa 'ya'yanku su da himma. Za ku haddace su sa'ad da kuke zaune a gida, da sa'ad da kuke tafiya, da sa'ad da kuke kwance, da sa'ad da kuka tashi.


Ku kula fa, kada ku ƙi mai maganar nan. Domin in waɗanda suka ƙi jin mai yi musu gargaɗi a duniya ba su tsira ba, to, ƙaƙa mu za mu tsira, in mun ƙi jin wannan da yake yi mana gargaɗi ma daga Sama?


Sai aka ji wata murya daga kursiyin, tana cewa, “Ku yabi Allahnmu, ya ku bayinsa, Ku da kuke jin tsoronsa, yaro da babba.”


Ku dai ku yi tsoron Ubangiji, ku bauta masa da aminci, da zuciya ɗaya. Ku tuna da manyan al'amuran da ya yi muku.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan