Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 32:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Bari koyarwata ta zubo kamar ruwan sama, Maganata ta faɗo kamar raɓa, Kamar yayyafi a bisa ɗanyar ciyawa, Kamar ɗiɗɗigar ruwa a bisa ganyaye.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Bari koyarwata tă zubo kamar ruwan sama kalmomina kuma su sauko kamar raɓa, kamar yayyafi a kan sabuwar ciyawa, kamar ruwan sama mai yawa a kan tsirai marasa ƙarfi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 32:2
14 Iomraidhean Croise  

Yana kama da hasken rana a kan girgijen alfijir, Rana da take sa ciyawa ta yi ƙyalƙyali bayan an gama ruwan sama.’


Ka kwarara ruwa mai yawa a gonakin da aka nome, Ka jiƙe su da ruwa, Ka tausasa ƙasar da yayyafi, Ka sa ƙananan tsire-tsire su yi girma.


Ka sa sarki ya zama kamar ruwan sama a gonaki, Ya zama kamar yayyafi a bisa ƙasa.


Abin da nake koya muku, abu mai kyau ne, saboda haka ku tuna da shi duka.


Zan zama kamar raɓa ga Isra'ila, Isra'ila za ta yi fure kamar lili, Saiwarta za ta shiga kamar itacen al'ul.


Ubangiji ya ce, “Me zan yi da ke, ya Ifraimu? Me zan yi da ke, ya Yahuza? Ƙaunarku tana kama da ƙāsashi, Kamar kuma raɓar da take watsewa da wuri.


Domin haka, sai ka kasa kunne ga abin da Ubangiji ya ce. Saboda ka ce mini in daina yin annabci gāba da jama'ar Isra'ila, kada kuwa in yi wa zuriyar Ishaku ɓaɓatu,


Za su mallaki ƙasar Assuriya da takobi, Su shiga ƙofofin ƙasar Nimrod da zararren takobi, Zai cece mu daga hannun Ba'assuriye, Sa'ad da ya kawo wa ƙasarmu yaƙi, Sa'ad da kuma ya tattake ƙasarmu.


Sa'an nan ringin Yakubu zai zamar wa mutane Kamar raɓa daga wurin Ubangiji, Kamar kuma yayyafi a kan tsire-tsire, Wanda ba ya jinkiri ko ya jira mutane.


Ku roƙi ruwan sama daga wurin Ubangiji a lokacin bazara, Gama Ubangiji ne yake yin gizagizan hadiri, Shi ne yake bai wa mutane yayyafi. Shi ne kuma yake ba kowane mutum tsire-tsiren saura.


Ƙasa ma da take shanye ruwan da ake yi mata a kai a kai, take kuma fid da tsire-tsire masu amfani ga waɗanda ake noma ta dominsu, Allah yakan sa mata albarka.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan