Amaryata, ki taho daga Dutsen Lebanon, Taho daga Lebanon. Ki taho daga ƙwanƙolin Dutsen Amana, Da Dutsen Senir da Harmon, Inda zakuna da damisoshi suke zaune.
tun daga Dutsen Halak wanda ya miƙa zuwa wajen Seyir, har zuwa Ba'al-gad a kwarin Lebanon, a gindin Dutsen Harmon. Ya kama sarakunan wuraren nan, ya buge su ya kashe su.