Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 3:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Dukan garuruwan nan masu dogo garu ne, da ƙofofi masu ƙyamaren ƙarfe. Banda waɗannan kuma akwai garuruwa da yawa marasa garu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Dukan biranen nan masu katanga da suke da tsayi masu ƙofofi da ƙyamare, akwai kuma manya ƙauyukan da ba su da katanga.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 3:5
8 Iomraidhean Croise  

Sun ci birane masu garu, da ƙasa mai dausayi, Da gidaje cike da dukiya, da rijiyoyi, da gonakin inabi, Da itatuwan zaitun, da itatuwa masu 'ya'ya. Suka ci dukan abin da suke so, suka yi taiɓa, Suka mori dukan kyawawan abubuwan da ka ba su.


Yahudawan da suke zaune a ƙauyuka, da karkara, suka mai da rana ta goma sha huɗu ga watan Adar, ranar farin ciki, da biki, da hutu, da ranar aika wa juna da abinci.


Amma mazaunan ƙasar ƙarfafa ne, biranenta kuma manya ne, masu garu, banda wannan kuma, mun ga Anakawa a can.


Ta ƙaƙa za mu hau? Gama 'yan'uwanmu sun narkar da zuciyarmu da cewa, mutanen sun fi mu girma, sun kuma fi mu ƙarfi. Biranensu kuma manya manya ne, da gine-gine masu tsayi ƙwarai. Har ma sun ga Anakawa a wurin.’


Muka ƙwace dukan garuruwansa a wannan lokaci. Ko gari guda ɗaya, ba mu bar musu ba, garuruwa sittin, da dukan yankin Argob, da mulkin Og a Bashan.


Muka hallaka su ƙaƙaf kamar yadda muka yi da Sihon, Sarkin Heshbon. Muka hallaka kowane gari, da mata da maza, da yara.


Ta wurin bangaskiya garun Yariko ya rushe, bayan an yi ta kewaya shi har kwana bakwai.


Suka kai siffofin ɓerayen nan na zinariya kuwa domin garuruwa biyar masu garu da ƙauyuka marasa garu na sarakunan Filistiyawa. Babban dutse inda suka ajiye akwatin Ubangiji yana nan har wa yau a saurar Joshuwa Bet-shemesh.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan