Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 3:12 - Littafi Mai Tsarki

12 “Sa'ad da muka mallaki ƙasar a wannan lokaci, sai na ba Ra'ubainawa da Gadawa yankin ƙasar daga Arower wadda take gefen kwarin kogin Arnon, da rabin ƙasar tuddai ta Gileyad tare da garuruwanta.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

12 Cikin ƙasar da muka kwasa a lokacin, na ba wa mutanen Ruben da mutanen Gad yankin arewa na Arower ta Kwarin Arnon, haɗe da rabin ƙasar tudu ta Gileyad, tare da biranenta.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 3:12
10 Iomraidhean Croise  

tun daga Urdun har zuwa wajen gabas, da dukan ƙasar Gileyad, da ta Gad, da ta Ra'ubainu, da ta Manassa, tun daga Arower wadda dake kusa da kwarin Arnon haɗe da Gileyad da Bashan.


Sai Musa ya ba mutanen Makir, ɗan Manassa, Gileyad, suka zauna ciki.


Daga Arower wadda take gefen kwarin kogin Arnon, zuwa Gileyad har ma da garin da yake cikin kwarin, Ubangiji Allahnmu ya ba da dukan kome a gare mu. Ba birnin da ya gagare mu.


Sa'ad da kuka isa wannan wuri, sai Sihon Sarkin Heshbon, da Og, Sarkin Bashan, suka fito su yi yaƙi da mu, amma muka ci su.


Muku ƙwace ƙasarsu, muka ba Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin kabilar Manassa, su gāda.


Sauran ƙasar Gileyad, da dukan ƙasar Bashan wadda take ƙarƙashin mulkin Og, wato dukan yankin ƙasar Argob.” (Duk dai yankin ƙasan nan wadda ake kira ƙasar Refayawa.) “Na ba da ita ga rabin kabilar Manassa.”


Ƙasar ta kama daga Arower wanda yake a kwarin kogin Arnon zuwa dutsen Siriyon, wato Harmon,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan