Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 3:11 - Littafi Mai Tsarki

11 (Sai Og, Sarkin Bashan, ne kaɗai ya ragu daga cikin Refayawa. Gadonsa na ƙarfe ne. Gadon yana nan a Rabbah ta Ammonawa. Tsawonsa kamu tara, faɗinsa kuma kamu huɗu ne.)

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 (Og sarkin Bashan, ne kaɗai ya ragu cikin Refahiyawa. An yi gadonsa da ƙarfe, tsawon gadon ya fi ƙafa goma sha uku, fāɗinsa kuwa ƙafa shida ne. Yana nan a Rabba ta Ammonawa har yanzu.)

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 3:11
15 Iomraidhean Croise  

A shekara ta goma sha huɗu Kedarlayomer da sarakunan da suke tare da shi suka zo suka cinye Refayawa cikin Ashterotkarnayim, da Zuzawa cikin Ham, da Emawa cikin Filin Kiriyatayim,


Ga yadda za ka sassaƙa shi, tsawon jirgin ƙafa ɗari huɗu da hamsin, faɗinsa ƙafa saba'in da biyar, tsayinsa ƙafa arba'in da biyar.


Da bazara lokacin da sarakuna sukan fita zuwa yaƙi, Dawuda ya aiki Yowab, da shugabannin sojojinsa, da sojojin Isra'ila duka. Suka tafi suka ragargaza Ammonawa, suka kuma kewaya Rabba da yaƙi. Amma Dawuda ya yi zamansa a Urushalima.


Yowab kuwa ya yi yaƙi da Rabba ta Ammonawa, yana kuwa gab da cin birnin.


Domin haka lokaci yana zuwa, Sa'ad da zan sa mutanen garin Rabba ta Ammon su ji busar yaƙi. Rabba za ta zama kufai, Za a ƙone ƙauyukanta da wuta, Sa'an nan Isra'ila zai mallaki waɗanda suka mallake shi. Ni Ubangiji na faɗa.


Ka nuna wa takobin hanya zuwa Rabba ta Ammonawa, da hanya zuwa Yahuza, da Urushalima, birni mai garu.


Zan mai da Rabba makiyayar raƙuma, in mai da biranen Ammonawa garken awaki da tumaki. Sa'an nan ku sani ni ne Ubangiji Allah.”


Saboda haka zan aukar da wuta a kan garun Rabba, Ta ƙone kagarar birnin. Za a yi kururuwa a ranar yaƙi, Faɗan kuwa zai yi rugugi kamar hadiri.


“Amma ga shi, saboda ku na hallakar da Amoriyawa, Dogayen mutanen nan masu kama da itatuwan al'ul, Ƙarfafa kuma kamar itatuwan oak, Na hallaka su ƙaƙaf.


Su ma akan lasafta su Refayawa tare da Anakawa, amma Mowabawa suka ce da su Emawa.


(Ita ma aka lasafta ta ƙasar Refayawa ce. Dā Refayawa waɗanda Ammonawa suke kira Zuzawa, su ne suka zauna cikinta.


da kuma Og, Sarkin Bashan, ɗaya daga cikin sauran Refayawa, wato gwarzayen nan waɗanda suka zauna a Ashtarot da Edirai.


da dukan mulkin Og a Bashan, wanda ya yi sarautar Ashtarot da Edirai (Og Kaɗai ne aka bari daga cikin Refayawa). Waɗannan su ne Musa ya ci da yaƙi, ya kore su.


Ya kuma auna garunsa, kamu ɗari da arba'in da huɗu ne na mutum, wato, na mala'ika ke nan.


Akwai wani jarumi, sunansa Goliyat, ya fito daga sansanin Filistiyawa. Tsayinsa kamu shida da rabi.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan