Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 3:10 - Littafi Mai Tsarki

10 “Wato dukan garuruwa na ƙasar tudu, da dukan ƙasar Gileyad, da ta Bashan har zuwa Salka da Edirai, garuruwa na mulkin Og ke nan cikin ƙasar Bashan.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Muka kama dukan biranen da suke kan tudu, da dukan Gileyad, da dukan Bashan, har zuwa Saleka da Edireyi, biranen masarautar Og a Bashan.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 3:10
10 Iomraidhean Croise  

'Ya'yan Gad, maza, suka zauna a ƙasar Bashan, daura da Ra'ubainawa har zuwa Salka.


Suka juya suka haura ta hanyar Bashan. Sai Og, Sarkin Bashan, da dukan jama'arsa suka fita, suka yi yaƙi da su a Edirai.


Biranen su ne, Bezer cikin jeji a kan tudu domin Ra'ubainawa, da Ramot cikin Gileyad domin Gadawa, da Golan cikin Bashan domin Manassawa.


da dukan Araba a hayin gabashin Urdun, har zuwa tekun Araba a gindin gangaren Fisga.


Nasu yankin ƙasar ya miƙa daga Arower wadda take a gefen kwarin Arnon, da birnin da yake tsakiyar kwarin, da dukan ƙasar tudu kusa da Medeba,


Yankin ƙasarsu ya bi daga Mahanayim, ya haɗa dukan Bashan, da dukan mulkin Og, Sarkin Bashan, da dukan garuruwan Yayir guda sittin da suke a Bashan,


da rabin Gileyad, da Ashtarot, da Edirai, wato garuruwan sarki Og a Bashan. Mutanen Makir ne, ɗan Manassa, aka ba su wannan bisa ga iyalansu.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan