Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 3:1 - Littafi Mai Tsarki

1 “Muka ci gaba da tafiyarmu muka nufi Bashan. Sai Og, Sarkin Bashan, tare da dukan jama'arsa suka fito su yi yaƙi da mu a Edirai.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Biye da wannan muka juya muka haura ta hanyar wajen Bashan, inda Og, sarkin Bashan tare da dukan mayaƙansa suka fito don su sadu da mu a yaƙi, a Edireyi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 3:1
15 Iomraidhean Croise  

“Ka sa sun ci al'ummai da mulkoki da yaƙi, Ƙasashen da suke maƙwabtaka da tasu. Suka ci ƙasar Sihon, Sarkin Heshbon, Da ƙasar Bashan, inda Og yake sarki.


Ya kashe Og, Sarkin Bashan, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.


A lokacin kuwa ya riga ya ci Sihon, Sarkin Amoriyawa, wanda yake zaune a Heshbon, da Og, Sarkin Bashan, wanda yake zaune a Ashtarot, da Edirai.


Sai Sihon da mutanensa suka fita su gabza yaƙi da mu a Yahaza.


Sa'ad da kuka isa wannan wuri, sai Sihon Sarkin Heshbon, da Og, Sarkin Bashan, suka fito su yi yaƙi da mu, amma muka ci su.


Sai Ubangiji ya ce mini, ‘Kada ka ji tsoronsu, gama da shi, da jama'arsa duka, da ƙasarsa, zan bashe su a hannunka. Sai ka yi masa kamar yadda ka yi wa Sihon, Sarkin Amoriyawa, wanda yake zaune a Heshbon.’


Ubangiji zai yi musu kamar yadda ya yi wa Sihon da Og, sarakunan Amoriyawa, da ƙasarsu, sa'ad da ya hallaka su.


Suka mallaki ƙasar Sihon, da ƙasar Og, Sarkin Bashan, sarakuna biyu na Amoriyawa waɗanda suke a hayin gabashin Urdun.


Waɗannan su ne sarakunan ƙasar, waɗanda Isra'ilawa suka cinye da yaƙi, suka mallaki ƙasarsu a hayin Kogin Urdun daga yamma, tun daga kwarin Arnon har zuwa Dutsen Harmon da dukan Araba a wajen gabas,


da kuma Og, Sarkin Bashan, ɗaya daga cikin sauran Refayawa, wato gwarzayen nan waɗanda suka zauna a Ashtarot da Edirai.


Yankin ƙasarsu ya bi daga Mahanayim, ya haɗa dukan Bashan, da dukan mulkin Og, Sarkin Bashan, da dukan garuruwan Yayir guda sittin da suke a Bashan,


da dukan abin da ya yi wa sarakunan nan biyu na Amoriyawa waɗanda suke a hayin Urdun, wato Sihon, Sarkin Heshbon, da Og, Sarkin Bashan, wanda yake a Ashtarot.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan