Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 27:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Bayan da kuka haye Urdun, kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, sai ku kakkafa manyan duwatsu, ku yi musu shafe da farar ƙasa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Sa’ad da kuka haye Urdun zuwa cikin ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, ku kakkafa waɗansu manyan duwatsu, ku yi musu shafe da farar ƙasa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 27:2
16 Iomraidhean Croise  

Ko kuwa ya zana kalmomina da kurfi a kan dutse, Ya rubuta su don su tabbata har abada!


Zan ba su zuciya ɗaya, in kuma sa sabon ruhu a cikinsu. Zan kawar musu da zuciya ta dutse, in ba su zuciya mai taushi,


Zan ba ku sabuwar zuciya, in sa sabon ruhu a cikinku. Zan cire zuciya mai tauri daga gare ku, sa'an nan in sa muku zuciya mai taushi.


Gama za ku haye Urdun, ku shiga ƙasar da za ku mallaka, wadda Ubangiji Allahnku yake ba ku. Sa'ad da kuka mallake ta, kuka zauna a ciki,


“Sa'ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ku gāda, kuka mallake ta, kuka zauna cikinta,


Musa da dattawan Isra'ila suka umarci jama'a, suka ce, “Ku kiyaye dukan umarnai waɗanda na umarce ku da su yau.


Sai ku rubuta kalmomin wannan shari'a a kansu daidai lokacin da kuka haye ku shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, ƙasar da take mai yalwar abinci, kamar yadda Ubangiji Allahnku ya alkawarta wa kakanninku.


Sa'ad da kuka haye Urdun ɗin sai ku kakkafa waɗannan duwatsu a bisa Dutsen Ebal bisa ga umarnin da na yi muku yau. Ku yi musu shafe da farar ƙasa.


“Waɗannan su ne umarnai, da dokoki, da farillai waɗanda Ubangiji Allahnku ya umarce ni in koya muku domin ku kiyaye su a ƙasar da kuke hayewa zuwa ciki don ku mallake ta,


“Ku ji, ya Isra'ilawa, yau kuna kan haye Kogin Urdun, don ku kori al'ummai waɗanda suka fi ku yawa, sun kuwa fi ku ƙarfi. Suna da manyan birane masu dogon garu.


“Ku shiga zango, ku umarci jama'a, ku ce, ‘Ku shirya wa kanku guzuri, gama nan gaba da kwana uku za ku haye Kogin Urdun don ku mallaki ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku.’ ”


Da al'umma duka suka gama haye Urdun, sai Ubangiji ya ce wa Joshuwa,


Joshuwa ya gina wa Ubangiji Allah na Isra'ilawa bagade a bisa Dutsen Ebal.


Ya gina shi kamar yadda Musa bawan Ubangiji ya umarci Isra'ilawa, gama haka aka rubuta cikin Attaura ta Musa, aka ce, “Bagaden da aka yi da duwatsun da ba a sassaƙa ba, waɗanda ba mutumin da ya taɓa sa musu guduma.” A bisansa suka miƙa hadayu ta ƙonawa ga Ubangiji, da hadayu na salama.


A nan, a idon Isra'ilawa, Joshuwa ya kafa dokokin Musa a bisa duwatsun.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan