Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 26:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Sai Ubangiji ya fisshe mu daga Masar da dantsensa mai ƙarfi, mai iko, tare da bantsoro, da alamu, da mu'ujizai.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Sai Ubangiji ya fitar da mu daga Masar da hannu mai ƙarfi da kuma iko, da razana mai girma da kuma alamu banmamaki da al’ajabai.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 26:8
15 Iomraidhean Croise  

Isra'ilawa mutum wajen zambar ɗari shida maza (600,000), banda iyalansu, suka kama tafiya daga Ramases zuwa Sukkot.


A ranar da shekara arbaminya da talatin ɗin nan suka cika, a ran nan ne dukan rundunar Ubangiji suka fita daga ƙasar Masar.


A wannan rana ce Ubangiji ya fitar da Isra'ilawa runduna runduna daga ƙasar Masar.


Musa ya ce wa jama'a, “Ku kiyaye wannan rana da kuka fito daga Masar, daga gidan bauta, gama da hannu mai ƙarfi Ubangiji ya fitar da ku daga wurin. Daɗai, ba za ku ci abinci mai yisti ba.


Sai ka faɗa wa Isra'ilawa cewa, ‘Ni Ubangiji zan 'yantar da ku daga wulakancin nan da Masarawa suke yi muku. Zan kuɓutar da ku daga bautar Masarawa. Da ƙarfi zan aikata hukuntaina masu iko don in cece ku.


Ina Ubangiji yake wanda ya yi manyan al'amura da ikonsa ta wurin Musa, ya raba ruwan teku a gaban jama'arsa, domin ya yi wa kansa madawwamin suna?”


Ta wurin alamu da al'ajabai, da iko, da ƙarfi, da banrazana, ka fito da jama'arka Isra'ila daga ƙasar Masar.


Ubangiji ya aike shi ya aikata alamu da mu'ujizai a ƙasar Masar a gaban Fir'auna da dukan barorinsa, da dukan ƙasarsa.


Ya kuma aikata ayyuka masu iko, masu bantsoro a gaban dukan Isra'ilawa.


Ko kuma, da akwai wani allah wanda ya taɓa ƙoƙarin fitar da al'umma saboda kansa daga cikin tsakiyar wata al'umma ta wurin wahalai, da alamu, da mu'ujizai, da yaƙi, da nuna iko, da babbar razana kamar yadda Ubangiji Allahnku ya yi dominku a ƙasar Masar a kan idonku duka?


Ka tuna fa, dā kai bawa ne a ƙasar Masar, amma Ubangiji Allahnka ya fisshe ka da dantse mai iko, mai ƙarfi. Domin haka Ubangiji Allahnka ya umarce ka ka kiyaye ranar Asabar.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan