Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 26:7 - Littafi Mai Tsarki

7 Amma muka yi kuka ga Ubangiji Allah na kakanninmu. Ubangiji kuwa ya ji kukanmu, ya ga azabarmu, da wahalarmu, da zaluncin da ake yi mana.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Sai muka yi kuka ga Ubangiji Allahn kakanninmu, Ubangiji kuwa ya ji kukanmu, ya kuma azabar da muke sha, da wahalar da muke sha, da danniyar da suke yin mana.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 26:7
18 Iomraidhean Croise  

Allah kuwa ya ji muryar yaron, mala'ikan Allah kuma ya kira Hajaratu daga sama, ya ce mata, “Me yake damunki, Hajaratu? Kada ki ji tsoro gama Allah ya ji muryar yaron a inda yake.


Lai'atu fa ta yi ciki ta haifi ɗa, ta raɗa masa suna Ra'ubainu, gama ta ce, “Saboda Ubangiji ya dubi wahalata, hakika, yanzu mijina zai ƙaunace ni.”


Watakila Ubangiji zai dubi azabata, ya sāka mini da alheri saboda wannan zagin da aka yi mini yau.”


Ka juyo wurina ka yi mini jinƙai, Kamar yadda kakan yi wa masu ƙaunarka.


Ba ka bar magabtana su kama ni ba, Ka kiyaye ni.


Ku yi kira gare ni sa'ad da wahala ta zo, Zan cece ku, Ku kuwa za ku yabe ni.”


Ana nan, a kwana a tashi, sai Sarkin Masar ya rasu. Jama'ar Isra'ila suka yi nishi, suka yi kuka kuma saboda bautarsu, kukansu na neman gudunmawa ya kai gun Allah.


Allah ya dubi jama'ar Isra'ila, ya kuwa kula da su.


Yanzu fa, ga shi, kukan jama'ar Isra'ila ya zo gare ni. Na kuma ga wahalar da Masarawa suke ba su.


Dattawan kuwa suka gaskata. Sa'ad da suka ji Ubangiji ya ziyarci Isra'ilawa, ya kuma ga wahalarsu, sai suka sunkuya, suka yi masa sujada.


Yanzu na ji nishin Isra'ilawa, waɗanda Masarawa suka bautar, na kuwa tuna da alkawarina.


Ubangiji wanda ya halitta duniya, ya siffata ta, ya kafa ta, sunansa Ubangiji, ya ce,


Ya ce masa, “Gobe war haka zan aiko maka da wani mutum daga kabilar Biliyaminu, sai ka zuba masa mai, ka keɓe shi sarki bisa jama'ata Isra'ila. Zai ceci jama'ata daga hannun Filistiyawa, gama na ga azabar da jama'ata suke sha, gama na ji kukansu.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan