Suka kuwa naɗa musu shugabannin aikin gandu domin su wahalshe su da mawuyacin aiki. Aka sa su su gina wa Fir'auna biranen ajiya, wato Fitom da Ramases.
“Sa'ad da kuke yi wa matan Ibraniyawa hidimarku ta ungozomai, in kuka gan su durƙushe, in jariri ne suka haifa, sai ku yi masa sanadin mutuwa, in kuma jaririya ce, ku bar ta da rai.”
Fir'auna kuwa ya umarci dukan mutanensa ya ce, “Duk jaririn da aka haifa wa Ibraniyawa, sai ku jefa shi cikin Kogin Nilu, amma idan jaririya ce, ku bar ta da rai.”