Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 26:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Sa'an nan kuma sai ku hurta waɗannan kalmomi a gaban Ubangiji Allahnku, ku ce, ‘Ubana Ba'aramiye ne, mayawaci a dā. Ya gangara zuwa Masar yana da jama'a kima, ya yi baƙunci a wurin. Amma a can ya zama al'umma mai girma, mai iko, mai yawa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Sa’an nan za ku furta a gaban Ubangiji Allahnku cewa, “Mahaifina mutumin Aram ne mai yawo, ya gangara zuwa Masar da mutane kaɗan, ya zauna a can, ya kuma zama babban al’umma, mai iko da kuma mai yawa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 26:5
28 Iomraidhean Croise  

Zan kuwa maishe ka al'umma mai girma, zan sa maka albarka, in sa ka ka yi suna, domin ka zama sanadin albarka.


Amma za ka tafi ƙasata, daga cikin dangina ka auro wa ɗana Ishaku mata.”


Ishaku yana da shekara arba'in sa'ad da ya auri Rifkatu, 'yar Betuwel Ba'aramiye daga Fadan-aram 'yar'uwar Laban Ba'aramiye.


Isuwa dai ya ƙi jinin Yakubu saboda albarkar da mahaifinsa ya sa masa. Sai Isuwa ya ce a ransa, “Kwanakin makoki domin mahaifina suna gabatowa, sa'an nan zan kashe Yakubu ɗan'uwana.”


Da haka, Ishaku ya sallami Yakubu, ya kuwa tafi Fadan-aram wurin Laban, ɗan Betuwel Ba'aramiye ɗan'uwan Rifkatu, mahaifiyar Yakubu da Isuwa.


Yakubu kuwa ya yaudari Laban Ba'aramiye da bai sanar da shi zai gudu ba.


Amma Allah ya zo wurin Laban Ba'aramiye cikin mafarki da dad dare, ya ce masa, “Ka kula fa, kada ka ce wa Yakubu kome, ko nagari ko mugu.”


Abin da na zama ke nan, da rana na sha zafin rana, da dare kuwa na sha sanyi, ga rashin barci.


Ku ɗauki kuɗi riɓi biyu a hannunku, ku kuma ɗauki kuɗin da aka mayar muku a tayakanku, kila kuskure ne aka yi.


A nan zan cishe ka, gama akwai sauran shekara biyar masu zuwa na yunwa, don kada ka tsiyace, kai da iyalinka, da duk wanda yake tare da kai.” ’


Allah kuwa ya aike ni a gabanku, domin in cetar muku da ringi a duniya, in kuma rayar muku kuɓutattu masu yawa.


'Ya'yan Yusufu, maza, waɗanda aka haifa masa a Masar su biyu ne. Dukkan mutane na gidan Yakubu da suka zo Masar su saba'in.


Ta haka fa Isra'ila ya yi zamansa a ƙasar Masar a ƙasar Goshen, suka kuwa sami mahalli a cikinta suka hayayyafa suka riɓaɓɓanya ƙwarai.


Suka kuma ce wa Fir'auna, “Ranka ya daɗe, mun zo baƙunci ne cikin ƙasar, gama ba wurin kiwo domin garkunan bayinka, gama yunwa ta tsananta a ƙasar Kan'ana. Yanzu muna roƙonka, ka yarda wa bayinka su zauna a ƙasar Goshen.”


Amma ko da yake Masarawa sun ƙara tsananta musu, duk da haka sai suka ƙara ƙaruwa, suna ta yaɗuwa. Masarawa kuwa suka tsorata saboda Isra'ilawa.


Zuriyar Yakubu duka mutum saba'in ne, Yusufu kuwa, an riga an kai shi Masar.


Amma 'ya'yan Isra'ila suka hayayyafa, suka ƙaru ƙwarai, suka riɓaɓɓanya, suka ƙasaita ƙwarai da gaske, har suka cika ƙasar.


Kakanmu Yakubu ya gudu zuwa ƙasar Aram, A can Isra'ila ya yi barantaka saboda mace, Saboda mace ya yi kiwon tumaki.


Ta wurin annabi Ubangiji ya fito da mutanen Isra'ila daga Masar, Ta wurin annabi kuma ya kiyaye su.


Sai Yakubu ya tafi Masar. A can ma ya mutu, shi da kakanninmu.


gama Ubangiji ya riɓaɓɓanya ku, har yawanku ya kai kamar taurarin sama.


Kakanninku saba'in ne suka gangara zuwa Masar, amma yanzu Ubangiji Allahnku ya riɓaɓɓanya ku, kuka yi yawa kamar taurarin sama.”


“Sa'an nan firist ya karɓi kwandon daga gare ku ya sa shi kusa da bagaden Ubangiji Allahnku.


“Ubangiji ya ƙaunace ku, ya zaɓe ku, ba don kun fi sauran al'ummai yawa ba, gama ku ne mafiya ƙanƙanta cikin dukan al'ummai.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan