Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 26:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Ku je wurin firist wanda yake aiki a lokacin, ku ce, ‘Yau, na sakankance a gaban Ubangiji Allahnka, cewa na shiga ƙasar da Ubangiji ya rantse wa kakanninmu zai ba mu.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 ku faɗa wa firist da yake aiki a lokacin, “Na sakankance yau ga Ubangiji Allahnka, cewa na zo ƙasar da Ubangiji ya rantse zai ba wa kakanninmu.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 26:3
13 Iomraidhean Croise  

Zan ba ka, kai da zuriyarka a bayanka, ƙasar baƙuncinka, wato dukan ƙasar Kan'ana ta zama mallakarka har abada, ni kuwa zan zama Allahnsu.”


Ka yi baƙunci cikin wannan ƙasa, ni kuwa zan kasance tare da kai, zan sa maka albarka, gama a gare ka da zuriyarka ne na ba da waɗannan ƙasashe, zan kuwa cika rantsuwar da na yi wa Ibrahim mahaifinka.


Duba, na sa ƙasar a gabanku, sai ku shiga ku mallake ta, ƙasa wadda na rantse wa kakanninku, wato Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, cewa zan ba su, su da zuriyarsu a bayansu.’ ”


sai su biyu ɗin su zo a gaban Ubangiji, su tsaya a gaban firistoci da alƙalai waɗanda suke aiki a lokacin.


to, sai ku keɓe nunan fari na dukan amfanin ƙasa wanda kuka shuka a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku. Ku sa cikin kwando, ku tafi inda Ubangiji Allahnku zai zaɓa don ya tabbatar da sunansa.


“Sa'an nan firist ya karɓi kwandon daga gare ku ya sa shi kusa da bagaden Ubangiji Allahnku.


da yake kuma muna da Firist mai girma, mai mulkin jama'ar Allah,


To, a koyaushe, sai mu yi ta yabon Allah ta wurinsa, sadakar da muke miƙawa ke nan, wato mu yabe shi, muna ta ɗaukaka sunansa.


Irin babban firist wanda muke bukata ke nan, mai tsarki, marar aibu, marar cikas, keɓaɓɓe daga masu zunubi, ɗaukakke kuma birbishin sammai.


Ku kuma, kamar rayayyun duwatsu, bari a gina gida mai ruhu da ku, domin ku zama tsattsarkar ƙungiyar firistoci, da nufin ku miƙa hadayu na ruhu, abin karɓa ga Allah, ta wurin Yesu Almasihu,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan