Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 26:2 - Littafi Mai Tsarki

2 to, sai ku keɓe nunan fari na dukan amfanin ƙasa wanda kuka shuka a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku. Ku sa cikin kwando, ku tafi inda Ubangiji Allahnku zai zaɓa don ya tabbatar da sunansa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 sai ku ɗauki ’ya’yan fari na dukan amfanin gonar ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, ku zuba a kwando. Sa’an nan ku je wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa yă zama mazauni don Sunansa,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 26:2
33 Iomraidhean Croise  

Wani mutum ya zo daga Ba'alshalisha ya kawo wa annabi Elisha abinci na 'ya'yan fari, da dunƙule ashirin na sha'ir, da ɗanyun zangarkun hatsi. Sai Elisha ya ce wa baransa, ya ba ƙungiyar annabawa su ci,


Nan da nan da aka baza labarin umarnin ko'ina, sai jama'ar Isra'ila suka ba da nunan fari na hatsinsu, da ruwan inabi, da mai, da zuma, da amfanin gona duka, suka kuma kawo zaka mai yawa ta kowane irin abu.


Amma na zaɓi Urushalima domin sunana ya kasance a wurin, na kuma zaɓi Dawuda ya zama shugaban jama'ata Isra'ila.’


A ran nan aka sa mutanen da za su lura da ɗakunan ajiya, da sadakoki, da nunan fari, da zaka. Su ne za su tara nunan fari daga gonakin da suke kusa da garuruwa, bisa ga yadda doka ta ce, saboda firistoci da Lawiyawa, gama mutanen Yahuza sun yi murna saboda hidimar da firistoci da Lawiyawa suka yi.


Na kuma shirya yadda za a tara itace domin yin hadaya a kan kari, da kuma lokacin da za a kawo nunan fari. “Ya Allahna, ka tuna da ni, ka yi mini alheri.”


Za ku gina mini bagade na ƙasa. A kansa za ku miƙa mini hadayu na ƙonawa da na salama, da tumakinku da shanunku. A duk inda na sa a tuna da sunana zan zo wurinku in sa muku albarka.


“Kada ku yi jinkirin fitar da zakar amfanin gonarku ta hatsi da ta abin matsewa. “'Ya'yan farinku, maza, kuma za ku ba ni su.


Ku kuma yi idin nunan fari na amfanin gonakinku da kaka. Sa'an nan kuma za ku yi idin gama tattara amfanin gonakinku a ƙarshen shekara.


“Wajibi ne ku kawo mafi kyau daga cikin nunan fari na amfanin gonakinku a gidan Ubangiji Allahnku. “Kada ku dafa ɗan akuya cikin madarar uwarsa.”


“Sai ku kawo nunan farin amfanin gonarku a cikin gidan Ubangiji Allahnku. “Kada ku dafa ɗan akuya da madarar uwarsa.”


Isra'ila tsattsarka ce ta Ubangiji, Nunar fari ta girbina. Dukan waɗanda suka ci daga cikinki sun yi laifi, Masifa za ta auko miki. Ni Ubangiji, na faɗa.”


“Gama a kan dutsena ne mai tsarki, wato a bisa ƙwanƙolin dutsen Isra'ila, dukan mutanen Isra'ila za su bauta mini a ƙasar, a nan ne zan karɓe su. A nan kuma zan nemi sadake-sada-kenku, da hadayunku mafi kyau.


Dukan nunan fari, da kowace hadaya daga dukan hadayunku, za su zama na firistoci. Za ku ba firistoci tumun farinku don albarka ta kasance a gidajenku.


Daga cikinsa ba za su sayar ba, ko su musayar, ba kuma za su jinginar da wannan keɓaɓɓen yankin ƙasa ba, gama tsattsarka ne na Ubangiji.


Amma a iya kawo su kamar hadayar nunan fari ga Ubangiji, sai dai ba za a ƙona su a kan bagade ba, kamar hadaya ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi.


Idan za a yi hadaya ta gari daga cikin nunan fari ga Ubangiji, sai a miƙa hadaya ta nunan fari da ɗanyen hatsi wanda aka gasa aka ɓarza.


In curin farko tsattsarka ne, haka sauran gurasar ma. In kuma saiwa tsattsarka ce, haka rassan ma.


Ku kuma gai da ikilisiyar da take taruwa a gidansu. Ku gai da ƙaunataccena Abainitas, wanda yake shi ne ya fara bin Almasihu a ƙasar Asiya.


Banda haka ma, har mu kanmu da muka riga muka sami Ruhu Mai Tsarki, wanda yake shi ne nunan fari, a cikin abubuwan da za mu samu, muna nishi a ranmu, muna ɗokin cikar zamanmu na 'ya'yan Allah, wato, fansar jikin nan namu ke nan.


Amma ga hakika an ta da Almasihu daga matattu, shi ne ma nunan fari na waɗanda suka yi barci.


Amma kowanne bi da bi, Almasihu ne nunan fari, sa'an nan a ranar komowarsa, waɗanda suke na Almasihu.


A kowace ranar farko ta mako, kowannenku ya riƙa tanada wani abu, yana ajiyewa gwargwadon samunsa, kada sai na zo tukuna, a tara gudunmawa.


Sa'an nan sai ku yi Idin Makonni domin Ubangiji Allahnku. Za ku ba da sadaka ta yardar rai gwargwadon albarkar da Ubangiji Allahnku ya sa muku.


Sai kuma ku ba su nunan fari na hatsinku, da ruwan inabinku, da manku, da kuma gashin tumakinku wanda kuka fara sausaya.


“Sa'ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ku gāda, kuka mallake ta, kuka zauna cikinta,


Ku je wurin firist wanda yake aiki a lokacin, ku ce, ‘Yau, na sakankance a gaban Ubangiji Allahnka, cewa na shiga ƙasar da Ubangiji ya rantse wa kakanninmu zai ba mu.’


Bisa ga nufinsa ya kawo mu ta maganar gaskiya, domin mu zama kamar nunan fari na halittarsa.


Da jama'ar Isra'ila suka ci ƙasar, sai suka tattaru a Shilo inda suka kafa alfarwa ta sujada.


Waɗannan su ne waɗanda ba su taɓa ƙazantuwa da fasikanci ba, domin su tsarkaka ne. Su ne kuma suke bin Ɗan Ragon a duk inda ya je. Su ne kuma aka fanso daga cikin mutane a kan su ne nunan fari na Allah, da na Ɗan Ragon nan kuma,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan