Amma idan 'yar firist ɗin gwauruwa ce, ko sakakkiya, ba ta kuma da ɗa, ta kuwa koma gidan mahaifinta, sai ta ci daga cikin abincin mahaifinta kamar cikin kwanakin ƙuruciyarta. Amma wani dabam ba zai ci ba.
In kuwa shi, ko ita, marar ba da gaskiya ɗin yana son rabuwa, to, sai su rabu. A wannan hali, ɗan'uwa ko 'yar'uwa mai bi, ba tilas a kansu, domin Allah ya kira mu ga zaman lafiya.
“Idan mutum ya sami wata mata ya aura, amma idan ba ta gamshe shi ba saboda ya iske wani abu marar kyau game da ita, har ya ba ta takardar saki a hannunta, ya sallame ta daga gidansa,