Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 2:9 - Littafi Mai Tsarki

9 “Sai Ubangiji ya ce mini, ‘Kada ku dami Mowabawa, ko kuwa ku tsokane su, gama ba zan ba ku ƙasarsu ku mallake ta ba. Na riga na bayar da Ar ta zama mallakar zuriyar Lutu.’ ”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Sai Ubangiji ya ce mini, “Kada ku dami Mowabawa, ko ku tsokane su da yaƙi, gama ba zan ba ku wani sashe na ƙasarsu ba. Na ba da Ar ga zuriyar Lot, ta zama mallakarsu.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 2:9
13 Iomraidhean Croise  

“Yanzu kuma ga mutanen Ammon, da na Mowab, da na Dutsen Seyir, waɗanda ka hana Isra'ilawa su kai musu yaƙi sa'ad da suka fito daga ƙasar Masar, su ne mutanen da Isra'ila suka ƙyale, ba su hallaka su ba.


Assuriya ma ta haɗa kai da su, Haɗa kai ke nan mai ƙarfi da zuriyar Lutu.


Wannan shi ne jawabi a kan Mowab. Biranen Ar da Kir, an hallaka su dare ɗaya, ƙasar ta yi tsit, ba kowa.


da gangaren kwaruruka, wanda ya nausa zuwa garin Ar, ya kuma dangana da kan iyakar Mowab.”


Gama sojojin Sihon sun shiga kamar wuta, A wannan birni na Heshbon, Sun cinye Ar ta Mowab, Ta murƙushe tuddan Arnon.


Mowabawa kuwa suka ce wa dattawan Madayanawa, “Yanzun nan wannan taro zai lashe dukan abin da yake kewaye da mu kamar yadda sā yakan lashe ciyawar saura.” Don haka Balak ɗan Ziffor wanda yake sarautar Mowab a lokacin,


Kai dai ka yardar mini in bi in wuce kamar yadda zuriyar Isuwa, mazaunan Seyir, da Mowabawa, mazaunan Ar, suka yardar mini. Gama ina so in haye Urdun zuwa ƙasa wadda Ubangiji Allahnmu yake ba mu.’


kada ku tsokane su, gama ko wurin sa ƙafa a ƙasarsu ba zan ba ku ba, gama na riga na ba Isuwa ƙasar tuddai ta Seyir.


tare da amsa, ya ce, “Isra'ilawa ba su ƙwace ƙasar Mowab ko ta Ammonawa ba.


Sa'an nan suka aike da jakadu wurin Sarkin Edom, su roƙe shi ya bar su su wuce ta ƙasarsa. Amma Sarkin Edom bai yarda ba. Suka kuma aika wa Sarkin Mowab, shi ma bai yarda ba, don haka Isra'ilawa suka zauna a Kadesh.


“Sa'an nan suka ci gaba da tafiya ta cikin hamada. Suka zaga ƙasar Edom da ta Mowab. Da suka kai gabashin ƙasar Mowab, sai suka yi zango a bakin Kogin Arnon, amma ba su haye kogin ba, gama shi ne iyakar ƙasar Mowab.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan