Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 2:8 - Littafi Mai Tsarki

8 “Muka yi gaba, muka bar zuriyar Isuwa 'yan'uwan nan namu waɗanda suke zaune a ƙasar tuddai ta Seyir, muka bar hanyar Araba, da hanyar Elat da Eziyon-geber. Muka juya, muka nufi wajen jejin Mowab.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Saboda haka muka ci gaba, muka wuce ’yan’uwanmu, zuriyar Isuwa, wanda yake zama a Seyir. Muka bar hanyar Araba, wadda ta haura daga Elat da Eziyon Geber, muka nufi wajen hamadar Mowab.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 2:8
9 Iomraidhean Croise  

Sai Ubangiji ya ce mata, “Al'umma biyu suke a cikin mahaifarki, mutum biyu da za ki haifa, za su rabu da juna, ɗayan zai fi ɗayan ƙarfi, babban zai bauta wa ƙaramin.”


Sarki Sulemanu kuma ya yi jiragen ruwa a Eziyon-geber wadda take kusa da Elat, a bakin Bahar Maliya a ƙasar Edom.


Shi ne ya gina Elat, ya mai da ita ta Yahuza bayan rasuwar tsohonsa.


A lokacin nan kuma Sarkin Edom ya sāke ƙwace Elat, ya kori Yahudawa daga cikinta, Edomawa suka zo suka zauna a ciki har wa yau.


Isra'ilawa suka kama hanya daga Dutsen Hor zuwa Bahar Maliya don su kauce wa ƙasar Edom. Sai jama'a suka ƙosa da hanyar.


Da suka tashi daga Abrona, sai suka sauka a Eziyon-geber.


Waɗannan su ne zantuttukan da Musa ya faɗa wa dukan Isra'ilawa a hayin Urdun cikin jejin Araba daura da Suf, tsakanin Faran, da Tofel, da Laban, da Hazerot, da Dizahab.


“Sa'an nan suka ci gaba da tafiya ta cikin hamada. Suka zaga ƙasar Edom da ta Mowab. Da suka kai gabashin ƙasar Mowab, sai suka yi zango a bakin Kogin Arnon, amma ba su haye kogin ba, gama shi ne iyakar ƙasar Mowab.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan