Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 2:7 - Littafi Mai Tsarki

7 Gama Ubangiji Allahnku ya sa albarka a kan dukan ayyukan hannuwanku. Ya kuma san tafiye-tafiyenku cikin babban jejin nan. Ubangiji Allahnku yana tare da ku a shekara arba'in ɗin nan, ba ku rasa kome ba.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Ubangiji Allahnku ya albarkace ku cikin dukan aikin hannuwanku. Ya kiyaye ku cikin tafiyarku a duk fāɗin hamada. Waɗannan shekaru arba’in Ubangiji Allahnku ya kasance tare da ku, ba kuwa kun rasa wani abu ba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 2:7
31 Iomraidhean Croise  

Zan kuwa maishe ka al'umma mai girma, zan sa maka albarka, in sa ka ka yi suna, domin ka zama sanadin albarka.


Ubangiji ya sa wa maigidana albarka ƙwarai, ya kuwa zama babba, ya ba shi garkunan tumaki da na shanu, da azurfa da zinariya, da barori mata da maza, da raƙuma da jakai.


Ishaku ya yi shuka a waccan ƙasar, a shekaran nan kuwa ya girbe cikakken amfani. Ubangiji ya sa masa albarka,


Amma Laban ya ce masa, “Da za ka yarda mini, sai in ce, na fahimta bisa ga istihara, cewa Ubangiji ya sa mini albarka saboda kai.


Maigidansa kuwa ya ga Ubangiji yana tare da shi, Ubangiji kuma yakan sa albarka ga aikin hannuwansa duka.


Ubangiji ya sa wa gidan Bamasaren albarka sabili da Yusufu tun daga lokacin da Fotifar Bamasaren ya shugabatar da shi a bisa gidansa da dukan dukiyarsa. Albarkar Ubangiji na bisa dukan abin da yake da shi, na gida da na jeji.


Ka taimake su a jeji shekara arba'in, Ka ba su dukan abin da suke bukata, Ƙafafunsu ba su kumbura su yi musu ciwo ba.


Duk da haka Allah ya san kowane irin hali da nake ciki. Idan ya jarraba ni zai tarar ni tsattsarka ne.


Gama Ubangiji yana lura da al'amuran adalai, Amma al'amuran mugaye za su watse.


Waɗansu suka yi ta kai da kawowa a hamada inda ba hanya, Sun kasa samun hanyar da za ta kai su garin da za su zauna a ciki.


Zan yi murna da farin ciki, Saboda madawwamiyar ƙaunarka. Ka ga wahalata, Ka kuwa san damuwata.


Ka yarda, albarkarka ta kasance tare da mu, ya Ubangiji Allahnmu. Ka sa mu yi nasara game da dukan abin da za mu yi! I, ka ba mu nasara a dukan abin da muke yi!


Shekara arba'in Isra'ilawa suka yi suna cin manna, har suka kai ƙasar da take da mutane, suka ci manna, har zuwa kan iyakar ƙasar Kan'ana.


in tafi in yi shelar abin da Ubangiji ya ce a kunnen Urushalima, in ce, “Na tuna da amincinki a lokacin ƙuruciyarki, Da ƙaunarki kamar ta amarya da ango. Yadda kika bi ni a cikin jeji, da a ƙasar da ba a shuka ba.


Ni ne wanda ya san ku a cikin jeji, A ƙasar da take da ƙarancin ruwan sama.


Na fito da ku, wato jama'ata daga Masar. Na bi da ku cikin jeji shekara arba'in, Na kuwa ba ku ƙasar Amoriyawa ta zama taku.


A rana ta fari ga wata na biyu a shekara ta biyu bayan da Isra'ilawa suka bar Masar, Ubangiji ya yi magana da Musa a cikin alfarwa ta sujada a jejin Sinai. Ya ce,


'Ya'yanku za su yi yawo a jeji shekara arba'in, za su sha wahala saboda rashin bangaskiyarku, har mutuminku na ƙarshe ya mutu a jejin.


Bisa ga kwanakin nan arba'in da kuka leƙi asirin ƙasar, haka za ku ɗauki alhakin zunubanku shekara arba'in, gama kowane kwana a maimakon shekara yake. Ta haka za ku sani ban ji daɗin abin da kuka yi ba.


Allah kuwa ya ce wa Bal'amu, “Ba za ka tafi tare da su ba, ba kuwa za ka la'anta su ba, gama albarkatattu ne su.”


Saboda Ubangiji ya husata da isra'ilawa, shi ya sa suka yi ta yawo a jeji har shekara arba'in, wato sai da tsaran nan wadda ta aikata mugunta a gaban Ubangiji ta ƙare.


Ya kuma ce musu, “Sa'ad da na aike ku ba kuɗi a ɗamararku, ba burgami, ba takalma, akwai abin da kuka rasa?” Suka ce, “Babu.”


Tumakin nan nawa sukan saurari muryata, na san su, suna kuma bi na.


“Sai muka tashi daga Horeb, muka ratsa babban jejin nan mai bantsoro wanda kuka gani a hanyarmu zuwa ƙasar tuddai ta Amoriyawa, kamar yadda Ubangiji Allahnmu ya umarce mu, muka zo Kadesh-barneya.


Kun kuwa zauna cikin Kadesh kwana da kwanaki, kamar dai yadda kuka yi.”


Lokacin da muka tashi daga Kadesh-barneya zuwa lokacin da muka haye rafin Zered, shekara talatin da takwas ne. Duk wannan lokaci dukan waɗanda suka isa yaƙi suka murmutu kamar yadda Ubangiji ya rantse a kansu.


Za ku sayi abincin da za ku ci, da ruwan da za ku sha a wurinsu.


Duk da haka har wa yau Ubangiji bai ba ku zuciyar ganewa, ko idanun gani, ko kunnuwan ji ba.


Shekara arba'in na bi da ku cikin jeji. Rigunanku da takalmanku ba su tsufa ba.


Gama shekara arba'in Isra'ilawa suna ta tafiya a jeji, har dukan al'umma, har da mayaƙan da suka fito daga Masar, suka hallaka, domin ba su kula da muryar Ubangiji ba. A gare su kuwa Ubangiji ya rantse, ba zai bar su su ga ƙasar da ya rantse wa kakanninsu zai ba su ba, ƙasar da take mai yalwar abinci.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan