Amma mutanen Isra'ila suka amsa musu suka ce, “Ai, za mu bi gwadabe ne kawai, idan kuwa mu da dabbobinmu mun sha ruwanku, sai mu biya, mu dai, a yardar mana mu wuce kawai.”
Gama Ubangiji Allahnku ya sa albarka a kan dukan ayyukan hannuwanku. Ya kuma san tafiye-tafiyenku cikin babban jejin nan. Ubangiji Allahnku yana tare da ku a shekara arba'in ɗin nan, ba ku rasa kome ba.’