Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 2:11 - Littafi Mai Tsarki

11 Su ma akan lasafta su Refayawa tare da Anakawa, amma Mowabawa suka ce da su Emawa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 Kamar Anakawa, su ma an ɗauka su Refahiyawa ne, amma Mowab suna kiransu Emawa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 2:11
10 Iomraidhean Croise  

A shekara ta goma sha huɗu Kedarlayomer da sarakunan da suke tare da shi suka zo suka cinye Refayawa cikin Ashterotkarnayim, da Zuzawa cikin Ham, da Emawa cikin Filin Kiriyatayim,


A waɗannan kwanaki kuwa, 'ya'yan Allah suka shiga wurin 'yan matan mutane, suka kuwa haifa musu 'ya'ya. Su ne manya manyan mutanen dā, shahararru.


Sai Ishbi-benob, ɗaya daga cikin Refayawa, gwarzayen nan, wanda nauyin mashinsa ya yi shekel ɗari uku na tagulla, yana kuma rataye da sabon takobi, ya zaci zai iya kashe Dawuda.


Suka haura ta wajen Negeb, suka isa Hebron inda Ahimaniyawa, da Sheshaiyawa, da Talmaiyawa, zuriyar ƙarfafan mutanen da ake kira Anakawa suke zaune. (An gina Hebron da shekara bakwai kafin a gina Zowan a Masar.)


Amma mazaunan ƙasar ƙarfafa ne, biranenta kuma manya ne, masu garu, banda wannan kuma, mun ga Anakawa a can.


Mun kuma ga manyan mutane a can, wato mutanen Anakawa da suka fito daga Nefilawa. Sai muka ga kanmu kamar fara ne kawai, haka kuwa muke a gare su.”


Ta ƙaƙa za mu hau? Gama 'yan'uwanmu sun narkar da zuciyarmu da cewa, mutanen sun fi mu girma, sun kuma fi mu ƙarfi. Biranensu kuma manya manya ne, da gine-gine masu tsayi ƙwarai. Har ma sun ga Anakawa a wurin.’


(Ita ma aka lasafta ta ƙasar Refayawa ce. Dā Refayawa waɗanda Ammonawa suke kira Zuzawa, su ne suka zauna cikinta.


(Sai Og, Sarkin Bashan, ne kaɗai ya ragu daga cikin Refayawa. Gadonsa na ƙarfe ne. Gadon yana nan a Rabbah ta Ammonawa. Tsawonsa kamu tara, faɗinsa kuma kamu huɗu ne.)


Mutane ne ƙarfafa, dogaye, zuriyar Anakawa waɗanda kuka riga kuka ji labarinsu. Ai, kun ji akan ce, ‘Wane ne zai iya tsayayya da 'ya'yan Anak?’


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan