Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 19:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Sai ku shirya hanyoyi, ku kuma raba yankin ƙasa wanda Ubangiji Allahnku zai ba ku ku mallaka kashi uku, domin wanda ya yi kisankai ya gudu zuwa can.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Ku gina hanyoyi zuwa cikinsu, ku kuma raba ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku gādo kashi uku, saboda duk wani da ya yi kisankai yă iya gudu zuwa can.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 19:3
8 Iomraidhean Croise  

Za a yi babbar karauka a can, Za a kira ta, “Hanyar Tsarki.” Ba mai zunubi da zai taɓa bi ta wannan hanya, Ba wawayen da za su ruɗar da waɗanda suke tafiya can.


Ubangiji ya ce, “Ku gina, ku shirya hanya. Ku kawar da kowane abin sa tuntuɓe daga kan hanyar jama'ata!”


Ku mutanen Urushalima, ku fita daga cikin birni, Ku gyara hanyoyi domin jama'arku da suke komowa! Ku shirya babbar hanya, Ku kawar da duwatsu daga hanyar! Ku sa alama domin al'ummai su sani,


sai ku keɓe garuruwa uku a ƙasar da Ubangiji Allahnku ya ba ku, ku mallaka.


Wannan shi ne tanadi domin wanda ya yi kisankai, wato wanda zai gudu zuwa can don ya tsira. Idan ya kashe abokinsa ba da niyya ba, ba kuma ƙiyayya a tsakaninsu a dā,


“Sa'ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ku gāda, kuka mallake ta, kuka zauna cikinta,


Amma Ubangiji ya yi fushi da ni sabili da ku, har ya rantse, cewa ba zan haye Urdun in shiga kyakkyawar ƙasan nan wadda yake ba ku abar gādo ba.


Ku bi miƙaƙƙun hanyoyi ɗoɗar, don kada mai ɗingishi ya gulle, a maimakon ya warke.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan