Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 17:3 - Littafi Mai Tsarki

3 har ya je, ya bauta wa gumaka, ya yi musu sujada, ko rana, ko wata, ko ɗaya daga cikin rundunar sama, ya yi abin da na hana,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 wanda ya saba wa umarnina, har ya yi sujada ga waɗansu alloli, yana rusuna musu, ko ga rana, ko ga wata, ko kuwa ga taurarin sama,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 17:3
14 Iomraidhean Croise  

Da haka aka gama yin sama da duniya, da rundunansu.


Gama ya gina matsafai a kan tuddai waɗanda Hezekiya tsohonsa ya rurrushe. Ya kuma gina wa Ba'al bagadai, ya kuma yi gunkiyan nan, wato Ashtoret, kamar yadda Ahab, Sarkin Isra'ila, ya yi. Ya yi wa taurari sujada, ya bauta musu.


“Wanda ya miƙa hadaya ga wani allah, ba ga Ubangiji ba, sai a hallaka shi ɗungum.


Sun gina wa Ba'al masujadai don su miƙa masa 'ya'yansu maza hadayar ƙonawa, abin da ban umarta ba, ban kuma ba da izni ba, ban ma yi tunanin haka ba.


Sun gina wa Ba'al masujadai a kwarin ɗan Hinnom don su miƙa 'ya'yansu mata da maza hadaya ga Molek, ni kuwa ban umarce su ba, ba shi kuwa a tunanina. Ga shi, sun aikata wannan abin banƙyama, don su sa Yahuza ta yi zunubi.”


A cikin kwarin ɗan Hinnon sun gina bagade, mai suna Tofet, don su miƙa 'ya'yansu mata da maza hadayar ƙonawa. Ni ban umarce su su yi haka ba, irin wannan abu ba shi a zuciyata.


Za a shimfiɗa su a rana, da a farin wata, da a gaban dukan rundunan sama, waɗanda suka ƙaunata, suka bauta wa, waɗanda suka nemi shawararsu, suka yi musu sujada. Ba za a tattara su a binne ba, amma za su zama juji a bisa ƙasa.


Ya kuma kai ni farfajiya ta can cikin Haikalin Ubangiji. Na ga mutum wajen ashirin da biyar a ƙofar Haikalin Ubangiji a tsakanin shirayi da bagade, suka juya wa Haikalin Ubangiji baya, suka fuskanci wajen gabas, suna yi wa rana sujada.


Ku lura fa, kada zuciya ta ruɗe ku, har ku kauce, ku bauta wa waɗansu alloli, ku yi musu sujada,


idan aka faɗa muku, ko kuwa kun ji labarinsa sai ku yi cikakken bincike. Idan gaskiya ce, aka kuma tabbata an yi wannan mugun abu cikin Isra'ilawa,


Ku lura fa, sa'ad da kuka dubi sama, kuka ga rana, da wata, da taurari, da dai dukan rundunar sama, don kada fa ku jarabtu, ku yi musu sujada, ko ku bauta musu. Ubangiji Allahnku ya sa waɗannan saboda dukan al'ummai.


Lokacin da kuka karya alkawarin Ubangiji Allahnku da ya umarce ku, kuka tafi kuka bauta wa gumaka, kuka sunkuya musu, to, Ubangiji zai yi fushi da ku, zai kuwa hallaka ku daga ƙasa mai albarka da aka ba ku.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan