Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 16:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Kada a iske yisti a ƙasarku duka har kwana bakwai. Kada kuma ku ajiye naman hadayar da kuka miƙa da yamma a rana ta fari ya kwana har safiya.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Kada a iske yisti a cikin mallakarku a dukan ƙasarku har kwana bakwai. Kada ku bar wani nama na hadayar da kuka yi a yammancin ranar farko, yă kwana har safe.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 16:4
9 Iomraidhean Croise  

Kada ku bar kome ya kai gobe, abin da ya kai gobe kuwa, sai ku ƙone shi.


“Za ku yi kwana bakwai kuna cin abinci marar yisti. A rana ta fari za ku fitar da yisti daga cikin gidajenku, gama duk wanda ya ci abin da aka sa wa yisti tun daga rana ta fari har zuwa ta bakwai za a fitar da shi daga cikin Isra'ila.


Za ku turke dabbar har rana ta goma sha huɗu ga wata, wato sa'ad da dukan taron jama'ar Isra'ila za su yanka ragunansu da maraice.


A daren nan za ku gasa naman, ku ci da abinci marar yisti, da ganyaye masu ɗaci.


Abinci marar yisti za a ci har kwana bakwai. Kada a ga wani da abinci mai yisti, ko kuma yisti ɗin kansa, a ko'ina a wurarenku.


“Kada ku miƙa jinin hadayata tare da abinci mai yisti. Kada kuma ku ajiye kitsen abin da aka yanka a lokacin idina, ya kwana.


“Ba za ku miƙa jinin hadayata tare da abinci mai yisti ba, kada kuma a bar hadaya ta Idin Ƙetarewa ta kwana.


Ya kuma ba su wani misali, ya ce, “Mulkin Sama kamar yisti yake, wanda wata mace ta ɗauka ta cuɗe da mudu uku na garin alkama, har duk garin ya game da yistin.”


“Kada ku miƙa hadayar ƙetarewa a kowane garin da Ubangiji Allahnku yake ba ku.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan