Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 16:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Kada ku ci abinci mai yisti tare da hadayar. Kwana bakwai za ku riƙa cin abinci marar yisti tare da hadayar, gama abincin wahala ne, gama da gaggawa kuka fita daga ƙasar Masar, don haka za ku tuna da ranar da kuka fito daga ƙasar Masar dukan kwanakinku.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Kada ku ci shi da burodin da aka yi da yisti, kwana bakwai za ku ci burodi marar yisti, burodi ne na wahala, gama kun bar Masar da gaggawa, saboda haka dukan kwanakin rayuwarku za ku tuna da lokacin da kuka fita daga Masar.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 16:3
27 Iomraidhean Croise  

Ku ce musu su jefa wannan mutum a kurkuku, a riƙa ciyar da shi da abinci kaɗan da ruwan sha kaɗan, har na komo lafiya.”


Toka ce abincina, Hawayena kuwa sun gauraya da abin shana,


Ubangiji ba zai bar mu mu manta da ayyukansa masu banmamaki ba, Shi mai alheri ne, mai jinƙai kuma.


Ba wani amfani a sha wahalar aiki saboda abinci, A yi asubancin tashi, a yi makarar kwanciya, Gama Ubangiji yakan hutar da waɗanda yake ƙauna.


Ga yadda za ku ci shi, da ɗamara a gindinku, da takalma a ƙafafunku, da sanda a hannunku, da gaggawa kuma za ku ci shi. Idin Ƙetarewa ne ga Ubangiji.


Za ku kiyaye idin abinci marar yisti, gama a wannan rana na fitar da rundunarku daga ƙasar Masar. Ku kiyaye wannan rana dukan zamananku. Wannan farilla ce ta har abada.


Suka toya abinci marar yisti da ƙullun da suka fita da shi daga Masar, gama ba su sa yisti cikin ƙullun ba domin an iza ƙyeyarsu, ba su sami damar dakatawa ba, ba su kuwa shirya wa kansu guzuri ba.


A daren nan za ku gasa naman, ku ci da abinci marar yisti, da ganyaye masu ɗaci.


“Sai ku kiyaye idin abinci marar yisti har kwana bakwai a ƙayyadadden lokacinsa a watan Abib, gama a watan Abib kuka fito Masar. A lokacin za ku ci abinci marar yisti kamar yadda na umarce ku.


A wannan lokaci ba za ku bukaci ku fita da garaje ba, Ba za ku yi ƙoƙari ku tsere ba! Ubangiji Allah ne zai bishe ku, Ya kuma kiyaye ku ta kowane gefe.


Sa'an nan kuma sha biyar ga watan za a yi bikin idin abinci marar yisti na Ubangiji. Za su ci abinci marar yisti har kwana bakwai.


“Zan cika zuriyar Dawuda da mutanen Urushalima da ruhun tausayi da na addu'a. Za su dubi wanda suka soke shi, har ya mutu. Za su yi makoki dominsa kamar waɗanda aka yi musu rasuwar ɗan farinsu.


Kashegari kuwa za a fara idin kwana bakwai. A kwanakin nan, sai a riƙa cin abinci marar yisti.


Za su kiyaye shi da maraice a watan biyu yana da kwana goma sha huɗu. Za su ci shi da abinci marar yisti da ganyaye masu ɗaci.


Sai ya ɗauki gurasa, bayan da ya yi godiya ga Allah, ya gutsuttsura, ya ba su, ya ce, “Wannan jikina ne da za a bayar dominku. Ku riƙa yin haka, domin tunawa da ni.”


Saboda haka, sai mu riƙa yin idinmu, ba da gurasa mai tsohon yisti ba, ba kuwa gauraye da yisti na ƙeta da na mugunta ba, sai dai da gurasa marar yisti ta sahihanci da ta gaskiya.


Sai ku miƙa hadayar ƙetarewa daga garkenku na tumaki da na shanu ga Ubangiji Allahnku a wurin da Ubangiji ya zaɓa domin ya tabbatar da sunansa.


“Sai ku lura, ku kiyaye kanku sosai, don kada ku manta da abubuwan da kuka gani da idonku kada kuma su fita a ranku dukan kwanakinku. Ku sanar wa 'ya'yanku da jikokinku da su,


har kuka zama masu koyi da mu, da kuma Ubangiji, kuka kuma karɓi Maganar Allah game da farin cikin da Ruhu Mai Tsarki yake sawa, ko da yake ta jawo muku tsananin wahala.


Sa'an nan za ku faɗa musu cewa, ‘Domin an yanke ruwan Urdun a gaban akwatin alkawari na Ubangiji sa'ad da ya haye Urdun.’ Waɗannan duwatsu za su zama abin tunawa ga Isra'ilawa har abada.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan