Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 16:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Sai ku miƙa hadayar ƙetarewa daga garkenku na tumaki da na shanu ga Ubangiji Allahnku a wurin da Ubangiji ya zaɓa domin ya tabbatar da sunansa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Ku miƙa ’yar dabba daga cikin garkenku na tumaki, ko na shanu a matsayin Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji Allahnku a wurin da Ubangiji zai zaɓa a matsayin mazauni don Sunansa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 16:2
19 Iomraidhean Croise  

Sarki Yosiya kuwa ya umarci dukan mutane, ya ce, “Ku kiyaye Idin Ƙetarewa ga Ubangiji Allahnku kamar yadda aka rubuta a littafin alkawari.”


Sarki Yosiya fa ya ba da gudunmawar abin yin hadaya ga waɗanda ba firistoci ba, waɗanda suke wurin, raguna da 'yan awaki daga cikin garken tumaki da na awaki, yawansu ya kai dubu talatin (30,000) da kuma bijimai dubu uku (3,000). Waɗannan duk daga mallakar sarki ne.


“Sai Isra'ilawa su kiyaye Idin Ƙetarewa a ƙayyadadden lokacinsa.


To, a ranar farko ta idin abinci marar yisti sai almajiran suka zo wurin Yesu suka ce, “Ina kake so mu shirya maka cin Idin Ƙetarewa?”


“Kun san Idin Ƙetarewa saura kwana biyu, za a kuma ba da Ɗan Mutum a gicciye shi.”


A ranar farko ta idin abinci marar yisti, wato ran da aka saba yanka ɗan ragon Idin Ƙetarewa, sai almajiransa suka ce masa, “Ina kake so mu je mu shirya maka cin Idin Ƙetarewa?”


Ya ce musu, “Ina so ƙwarai ko dā ma in ci jibin nan na Ƙetarewa tare da ku, kafin in sha wuya.


Sai Yesu ya aiki Bitrus da Yahaya, ya ce musu, “Ku je ku shirya mana Jibin Ƙetarewa mu ci.”


Ku fitar da tsohon yistin nan, don ku zama sabon curi, domin hakika an raba ku da yistin, da yake an riga an yanka Ɗan Ragonmu na Idin Ƙetarewa, wato, Almasihu.


sai ku kai dukan abin da na umarce ku ku kai, wato hadayu na ƙonawa, da sadakokinku, da zakarku, da hadayunku na ɗagawa, da hadayunku na wa'adi da kuka yi wa Ubangiji a wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa ya sa sunansa.


amma sai a wurin nan ɗaya wanda Ubangiji zai zaɓa daga cikin kabilanku, nan za ku miƙa hadayunku na ƙonawa, nan ne kuma za ku yi dukan abin da na umarce ku.


Amma sai ku ci su a inda Ubangiji Allahnku zai zaɓa, ku da 'ya'yanku mata da maza, da barorinku mata da maza, da Lawiyawa da suke a cikin garuruwanku. Sai ku yi murna a gaban Ubangiji Allah saboda duk abin da kuke yi.


Amma tsarkakakkun abubuwan da suke wajibanku da hadayunku na wa'adi, su ne za ku ɗauka ku kai wurin da Ubangiji ya zaɓa.


Amma sai ku nemi wurin da Ubangiji Allahnku zai zaɓa daga cikin kabilanku duka, inda zai sa sunansa, ya mai da shi wurin zamansa.


Ku da iyalanku za ku ci shi kowace shekara a gaban Ubangiji Allahnku a wurin da Ubangiji zai zaɓa.


“Ku kiyaye watan Abib don ku yi Idin Ƙetarewa ga Ubangiji Allahnku, gama a watan Abib ne Ubangiji Allahnku ya fito da ku daga Masar da dad dare.


Kada ku ci abinci mai yisti tare da hadayar. Kwana bakwai za ku riƙa cin abinci marar yisti tare da hadayar, gama abincin wahala ne, gama da gaggawa kuka fita daga ƙasar Masar, don haka za ku tuna da ranar da kuka fito daga ƙasar Masar dukan kwanakinku.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan