Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 15:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Ga yadda za ku yafe. Sai kowane mai bin bashi ya yafe wa maƙwabcinsa, kada ya karɓi kome a hannun maƙwabcinsa ko ɗan'uwansa, gama an yi shelar yafewa ta Ubangiji.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Ga yadda za ku yafe basusuwan, kowane mai bin bashi, yă yafe bashin da yake bin ɗan’uwansa mutumin Isra’ila. Ba zai bukaci mutumin Isra’ila wanda yake ɗan’uwa yă biya shi bashi ba, gama an yi shelar lokacin da Ubangiji ya ajiye na yafe bashi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 15:2
13 Iomraidhean Croise  

“Idan kuma mutanen ƙasar sun kawo kayayyaki da hatsi don sayarwa a ranar Asabar, ba za mu saya ba, ko kuma a wata tsattsarkar rana. “A kowace shekara ta bakwai ba za mu girbe amfanin gonakinmu ba, za mu kuma yafe kowane irin bashi.


Mutane sukan ce, “Me ya sa muka yi azumi, Ubangiji bai gani ba? Me ya sa muka ƙasƙantar da kanmu, Ubangiji kuwa bai kula ba?” Ubangiji ya ce musu, “Duba, a ranar da kuke azumi, nishaɗin kanku kuke nema, kuna zaluntar dukan ma'aikatanku.


Ka gafarta mana laifofinmu, Kamar yadda mu ma muke gafarta wa waɗanda suke yi mana laifi.


Da suka gagara biya, sai ya yafe musu dukansu biyu. To, a cikinsu wa zai fi ƙaunarsa?”


“A ƙarshen kowace shekara bakwai dole ku yafe dukan basusuwan da kuke bi.


Kana iya matsa wa baƙo ya biya ka, amma sai ka yafe wa danginka bashin da kake binsa.


Sai Musa ya umarce su, ya ce, “A ƙarshen kowace shekara bakwai, a lokacin da aka ƙayyade na shekarar yafewa, a lokacin Idin Bukkoki,


Gama Shari'a marar jinƙai ce ga wanda ba ya nuna jinƙai. Amma jinƙai yana rinjayar hukunci.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan