Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 13:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Sai a kashe annabin nan, ko mai mafarkin don ya koyar a tayar wa Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar, wato inda kuka yi bauta, gama ya yi ƙoƙari ya sa ku ku kauce daga hanyar da Ubangiji Allahnku ya umarce ku ku bi. Ta haka za ku kawar da mugunta daga cikinku.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Dole a kashe wannan annabi ko mai mafarki, domin ya yi wa’azin tawaye ga Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar, ya fanshe ku daga ƙasar bauta; gama annabin nan ya yi ƙoƙari yă juye daga hanyar da Ubangiji Allahnku ya umarce ku, ku bi. Dole ku fid da mugu daga cikinku.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 13:5
34 Iomraidhean Croise  

Saboda haka sai annabin ya koma tare da shi, ya ci abinci, ya sha ruwa a gidan tsohon annabin.


Iliya kuma ya ce musu, “Ku kama annabawan Ba'al, kada ku bar ko ɗaya ya tsere.” Iliya kuwa ya kai su rafin Kishon, ya karkashe su a can.


Sai sarkin ya miƙe tsaye a inda yake, ya yi alkawari a gaban Ubangiji, cewa zai bi Ubangiji, ya kiyaye umarnansa, da farillansa, da dokokinsa da zuciya ɗaya, da dukan ransa. Zai yi aiki da alkawarin da yake rubuce a wannan littafi.


Domin haka ga abin da ni Ubangiji na ce a kan annabawan da suke yin annabci da sunana, ko da yake ban aike su ba, waɗanda suke cewa, ‘Takobi da yunwa ba za su shigo ƙasan nan ba.’ Za a hallaka su da takobi da yunwa.


saboda haka Ubangiji ya ce, ‘ga shi, zan hukunta Shemaiya, mutumin Nehelam, shi da zuriyarsa ba za a bar masa mai rai ko ɗaya a wannan jama'a ba, wanda zai ga irin alherin da zan yi wa jama'ata, gama ya kuta tayarwa ga Ubangiji,’ ” in ji Ubangiji.


“Mutanena sun zama kamar ɓatattun tumaki, Waɗanda makiyayansu suka bauɗar da su, Suka ɓata a cikin tsaunuka, Suna kai da kawowa daga wannan dutse zuwa wancan. Sun manta da shingensu.


Amma na umarce su su yi biyayya da maganata, zan zama Allahnsu, su kuma za su zama mutanena, su bi dukan al'amuran da na umarce su, domin lafiyarsu, don su zama lafiya.


Idan har yanzu wani ya ci gaba da yin annabci, sai mahaifinsa da mahaifiyarsa su ce masa, ‘Ba za ka rayu ba, gama kana faɗar ƙarya da sunan Ubangiji.’ Sa'an nan mahaifinsa da mahaifiyarsa su soke shi sa'ad da yake annabcin.


Amma Alimas mai sihirin nan, (don wannan ita ce ma'anar sunansa), ya mūsa musu, yana neman bauɗar da muƙaddashin nan daga bangaskiya.


Allah ne yake hukunta waɗanda ba namu ba. Ku kori mugun nan daga cikinku.


Ku jajjefe shi da duwatsu har ya mutu, saboda ya yi niyyar janye ku daga bin Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar, wato inda kuka yi bauta.


sai ku karkashe dukan mazaunan garin da takobi, ku kuma karkashe dabbobin da suke cikinsa. Za ku hallaka garin ƙaƙaf.


Hannunku ne zai fara jifansa, sa'an nan sauran jama'a su jajjefe shi, har ya mutu.


to, ku kawo macen, ko mutumin, da ya aikata wannan mugun abu a bayan ƙofar garinku, nan za ku jajjefe shi da duwatsu har ya mutu.


Sai shaidun su fara jifansa sa'an nan sauran jama'a su jajjefe shi. Ta haka za a kawar da mugunta daga cikinsu.


Amma duk wani annabin da ya yi izgili yana magana da sunana, ni kuwa ban umarce shi ba, ko kuwa yana magana da sunan gumaka, wannan annabi zai mutu.’


to, sai ku yi masa kamar yadda ya so a yi wa wancan mutumin. Ta haka za ku kawar da mugunta daga cikinku.


sai a kai yarinyar a ƙofar gidan mahaifinta, sa'an nan mutanen garin su jajjefe ta da duwatsu har ta mutu, don ta yi aikin wauta cikin Isra'ila, gama ta yi karuwanci a gidan mahaifinta. Ta haka za ku kawar da mugunta daga cikinku.


sai a kawo su, su biyu ɗin, a dandalin ƙofar gari, ku jajjefe su da duwatsu har su mutu, don yarinyar tana cikin gari, amma ba ta yi kururuwa a taimake ta ba, don kuma mutumin ya ɓata budurwar maƙwabcinsa. Da haka za ku kawar da mugunta daga cikinku.


“Idan aka iske mutum yana satar danginsa Ba'isra'ile don ya maishe shi bawansa, ko ya sayar da shi, sai a kashe ɓarawon. Ta haka za ku kawar da mugunta daga tsakiyarku.


Ban ci kome daga cikin zakar sa'ad da nake baƙin ciki ba, ban kuma fitar da kome daga cikinta ba sa'ad da nake da ƙazanta, ban kuma miƙa wa matattu kome daga cikinta ba. Na yi biyayya da muryar Ubangiji Allahna, na aikata dukan abin da ka umarce ni.


Ku lura fa, sa'ad da kuka dubi sama, kuka ga rana, da wata, da taurari, da dai dukan rundunar sama, don kada fa ku jarabtu, ku yi musu sujada, ko ku bauta musu. Ubangiji Allahnku ya sa waɗannan saboda dukan al'ummai.


Sai ku ji tsoron Ubangiji Allahnku. Shi ne za ku bauta masa, ku rantse da sunansa.


Gama za su sa 'ya'yanku su bar bina, su bauta wa gumaka. Wannan zai sa Ubangiji ya husata, ya hallaka ku da sauri.


Amma ku manne wa Ubangiji Allahnku kamar yadda kuka yi har wa yau.


Sai aka kama dabbar, da kuma annabin nan na ƙarya tare da ita, wanda ya yi al'ajabai a gabanta, waɗanda da su ne ya yaudari waɗanda suka yarda a yi musu alamar dabbar nan, da kuma waɗanda suka yi wa siffarta sujada. Waɗannan biyu kuwa aka jefa su da ransu a cikin tafkin wuta da ƙibiritu.


Yanzu sai ku ba da mutanen nan 'yan iska da take cikin Gibeya don mu kashe su, mu kawar da mugunta daga cikin Isra'ila.” Amma mutanen Biliyaminu ba su kula da maganar 'yan'uwansu, Isra'ilawa ba.


Idan za ku yi tsoron Ubangiji, ku bauta masa, ku yi biyayya da maganarsa, ba za ku karya umarnin Ubangiji ba, idan kuma ku da sarkin da yake sarautarku za ku bi Ubangiji Allahnku, kome zai zamar muku daidai.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan