Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 13:3 - Littafi Mai Tsarki

3 kada ku saurari maganar annabin nan ko mai mafarkin nan, gama Ubangiji Allahnku yana jarraba ku ne, ya gani, ko kuna ƙaunarsa da zuciya ɗaya da dukan ranku.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 kada ku saurari kalmomin wannan annabi ko mai mafarki. Ubangiji Allahnku yana gwada ku ne don yă sani ko kuna ƙaunarsa da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 13:3
21 Iomraidhean Croise  

Saboda haka sai annabin ya koma tare da shi, ya ci abinci, ya sha ruwa a gidan tsohon annabin.


Masu farin ciki ne waɗanda suke bin umarnansa, Waɗanda suke yi masa biyayya da zuciya ɗaya.


Ka jarraba mu, ya Allah, Kamar yadda ake tace azurfa da wuta, Haka nan ka jarraba mu.


Sa'ad da kuke shan wahala Kuka yi kira a gare ni, na kuwa cece ku. Daga maɓuyata cikin hadiri, na amsa muku, Na jarraba ku a maɓuɓɓugan Meriba.


Musa kuwa ya ce wa jama'a, “Kada ku ji tsoro, gama Allah ya zo ne don ya jarraba ku, don ku riƙa girmama shi, don kuma kada ku yi zunubi.”


Ga amsar da za ku ba su, ku ce, “Ku kasa kunne ga koyarwar Ubangiji. Kada ku kasa kunne ga 'yan bori. Gama abin da suka faɗa muku ba zai amfane ku ba.”


Don almasihan ƙarya da annabawan ƙarya za su firfito, su nuna manyan alamu da abubuwan al'ajabi, don su ɓad da ko da zaɓaɓɓu ma in dai zai yiwu.


To, waɗannan Yahudawa kam, sun fi na Tasalonika dattaku, domin sun karɓi Maganar hannu biyu biyu, suna ta nazarin Littattafai kowace rana, su ga ko abin haka yake.


Don lalle ne a sami tsattsaguwa a tsakaninku, don a iya rarrabewa da waɗanda suke amintattu a cikinku.


Ba kallafa muku wannan nake yi ba, sai dai ta nuna himmar waɗansu, in tabbata ƙaunarku ma sahihiya ce.


An yi wannan kuwa don kada mu sāke zama kamar yara, waɗanda suke jujjuyawa, iskar kowace koyarwa tana ɗaukar hankalinsu, bisa ga wayon mutane da makircinsu da kissoshinsu.


Sai ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku da zuciya ɗaya, da dukan ranku, da dukan ƙarfinku.


Ya ciyar da ku da manna a jeji, abin da kakanninku ba su sani ba, domin ya koya muku tawali'u, ya jarraba ku, don ya yi muku alheri daga baya.


Ku tuna yadda Ubangiji Allahnku ya bishe ku shekarun nan arba'in a jeji don ya koya muku tawali'u. Ya jarraba ku don ya san zuciyarku, ko za ku kiyaye umarnansa ko babu.


Saboda haka, Allah zai auko musu da wata babbar ɓatan basira don su gaskata ƙarya,


Sun dai fita daga cikinmu, amma dā ma can ba namu ba ne. Don in da namu ne, da har yanzu suna tare da mu. Amma sun fita ne domin a bayyana dukansu ba namu a ciki.


Ya ku ƙaunatattuna, ba kowane ruhu za ku gaskata ba, sai dai ku jarraba ku gani ko na Allah ne, don annabawan ƙarya da yawa sun fito duniya.


Ya ku 'ya'yana ƙanana, ku kam na Allah ne, kun kuma ci nasara a kan waɗannan, domin shi wanda yake zuciyarku ya fi wanda yake duniya ƙarfi.


Tana kuma yaudarar mazaunan duniya, da abubuwan al'ajabin nan da aka yardar mata ta yi a gaban dabbar nan, tana umartarsu, su yi wata siffa saboda dabbar nan wadda aka yi wa rauni da takobi, ta kuwa rayu.


Da haka ne zan jarraba Isra'ilawa, in gani ko za su mai da hankali su yi tafiya cikin hanyata, kamar yadda kakanninsu suka yi, ko kuwa ba za su yi ba.”


Bari sarki ya kasa kunne ga maganar baransa. Idan Ubangiji ne ya kuta ka ka yi gāba da ni, to, bari ya karɓi hadaya, amma idan mutane ne, to, bari su zama la'anannu, gama sun kore ni don kada in sami rabo cikin gādon Ubangiji, suna cewa, ‘Tafi ka bauta wa alloli.’


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan