Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 13:2 - Littafi Mai Tsarki

2 idan alamar ko mu'ujizar ta auku, idan kuma ya ce, ‘Bari mu bi gumaka, mu bauta musu, gumakan da ba ku san su ba,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 in kuwa alamar, ko al’ajabin da annabin ya yi faɗin ya faru, ya kuma ce, “Bari mu bi waɗansu alloli (allolin da ba ku sani ba) mu kuma yi musu sujada,”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 13:2
16 Iomraidhean Croise  

Ya kuma ba da alama a wannan rana cewa, “Wannan ita ce alamar da Ubangiji ya faɗa, za a rushe bagaden, a zubar da tokar da take bisansa.”


“Duk wanda ya kwana da dabba, lalle kashe shi za a yi.


Masu sihiri kuma na Masar suka yi haka, su ma, ta wurin sihirinsu, don haka zuciyar Fir'auna ta daɗa taurarewa, ya kuwa ƙi jin Musa da Haruna kamar yadda Ubangiji ya riga ya faɗa.


Ina kuma gāba da annabawan da suke annabcin mafarkansu na ƙarya, suna kuwa faɗarsu suna ɓad da mutanena da ƙarairayinsu, saboda rashin hankalinsu. Ni ban aike su ba, ban kuwa umarce su ba. Ba su amfani wannan jama'a ba ko kaɗan, ni Ubangiji na faɗa.”


Saboda haka kada ku saurari annabawanku, da masu duba, da masu mafarkai, da matsubbata, ko masu sihiri waɗanda suka ce muku ba za ku bauta wa Sarkin Babila ba.


Idan maganar wannan annabi kuwa da ya yi annabcin salama ta cika, sa'an nan ne za a sani gaskiya Ubangiji ne ya aiko shi.”


Gama maganar shirme kan gida yake yi, Masu dūba suna ganin wahayin ƙarya, Masu mafarkai suna faɗar ƙarya, Ta'aziyyarsu ta banza ce. Domin haka mutane suna ta yawo kamar tumaki, Suna shan wahala saboda rashin makiyayi.


Don almasihan ƙarya da annabawan ƙarya za su firfito, su nuna manyan alamu da abubuwan al'ajabi, don su ɓad da ko da zaɓaɓɓu ma in dai zai yiwu.


“Idan ɗan'uwanka, wato ɗan mahaifiyarka, ko ɗanka, ko 'yarka, ko ƙaunatacciyar matarka, ko amininka ya rarrashe ka a asirce, yana cewa, ‘Bari mu tafi mu bauta wa gumaka waɗanda ku da ubanninku ba ku san su ba,’


Amma duk wani annabin da ya yi izgili yana magana da sunana, ni kuwa ban umarce shi ba, ko kuwa yana magana da sunan gumaka, wannan annabi zai mutu.’


Sa'ad da annabi ya yi magana da sunan Ubangiji, idan abin da ya faɗa bai faru ba, bai zama gaskiya ba, to, wannan magana ba Ubangiji ne ya faɗa ba. Wannan annabi ya yi izgili ne kawai, kada ku ji tsoronsa.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan