Ubangiji zai hukunta Isra'ila kamar yadda akan girgiza iwa a baƙin rafi, zai tumɓuke Isra'ila daga wannan ƙasa mai albarka wadda ya ba kakanninsu, ya kuma watsar da su a hayin Kogin Yufiretis, domin sun yi wa kansu gumaka don sun tsokani Ubangiji ya yi fushi.
Sai ku rurrushe bagadansu, ku ragargaje al'amudansu, ku ƙone ginshiƙansu na tsafi, ku kuma sassare siffofin gumakansu, ku shafe sunayensu daga wuraren nan.