Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 10:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Domin haka kabilar Lawi ba su da rabo ko gādo tare da 'yan'uwansu, Ubangiji shi ne gādonsu kamar yadda Ubangiji Allahnku ya faɗa musu.)

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Shi ya sa Lawiyawa ba su da rabo, ko gādo a cikin ’yan’uwansu; Ubangiji ne gādonsu yadda Ubangiji Allahnku ya faɗa musu.)

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 10:9
9 Iomraidhean Croise  

“Ba za su sami rabon gādo ba, gama ni ne rabon gādonsu. Ba za ku ba su abin mallaka a cikin Isra'ila ba, ni ne abin mallakarsu.


Mazan da aka ƙidaya daga mai wata guda zuwa gaba sun kai dubu ashirin da dubu uku (23,000). Ba a haɗa jimillarsu tare da ta sauran Isra'ilawa ba, da yake ba a ba su gādo tare da su ba.


Ba ruwanka da wannan al'amari sam, don zuciyarka ba ɗaya take ba a gaban Allah.


Ku yi murna a gaban Ubangiji Allahnku, ku da 'ya'yanku mata da maza, da barorinku mata da maza tare da Lawiyawa waɗanda suke zaune cikinku tun da yake ba su da rabo ko gādo tare da ku.


“Amma fa, kada ku manta da Balawen da yake garuruwanku gama ba shi da gādo kamarku.


Sa'an nan sai Balawe, da yake shi ba shi da gādo kamarku, da baƙo, da maraya, da gwauruwa ta gaske, waɗanda suke zaune a garuruwanku, su zo, su ci, su ƙoshi, domin Ubangiji Allahnku ya sa muku albarka cikin dukan aikin da hannunku zai yi.”


Gama Musa ya riga ya ba kabilan nan biyu da rabi nasu gādo a wancan hayin Kogin Urdun wajen gabas, amma bai ba Lawiyawa rabon gādo ba.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan