Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 10:8 - Littafi Mai Tsarki

8 A wannan lokaci ne Ubangiji ya keɓe kabilar Lawi domin su riƙa ɗaukar akwatin alkawari na Ubangiji, su kuma tsaya a gaban Ubangiji, su riƙa yi masa aiki, su kuma sa albarka da sunan Ubangiji kamar yadda yake a yau.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 A lokacin Ubangiji ya keɓe kabilar Lawi don su riƙa ɗaukar akwatin alkawarin Ubangiji, su tsaya a gaban Ubangiji, su riƙa yin masa hidima, su kuma sa albarka a cikin sunansa, yadda suke yi har wa yau.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 10:8
39 Iomraidhean Croise  

Sa'an nan firistoci suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji suka sa a cikin Wuri Mai Tsarki na can ciki a Haikalin, a ƙarƙashin fikafikan kerubobi.


Sai Dawuda ya ce, “Kada wani ya ɗauki akwatin alkawari na Allah sai Lawiyawa kaɗai, gama su ne Ubangiji ya zaɓa domin su riƙa ɗaukar akwatin alkawarin Ubangiji, su kuma yi masa hidima har abada.”


Saboda Allah ya taimaki Lawiyawa waɗanda suka ɗauki akwatin alkawarin Ubangiji, sai suka yi hadaya da bijimai bakwai da raguna bakwai.


'Ya'yan Amram, maza, su ne Haruna, da Musa. Aka keɓe Haruna domin ya tsarkake abubuwa mafi tsarki, domin shi da 'ya'yansa za su ƙone turare a gaban Ubangiji, su yi masa hidima, su riƙa sa albarka da sunansa har abada.


Yanzu Lawiyawa ba za su riƙa ɗaukar alfarwar sujada tare da kayayyakin yin aiki a cikinta ba.”


'Ya'yana, kada ku yi sakaci, gama Ubangiji ne ya zaɓe ku don ku tsaya a gabansa, ku yi masa hidima, ku ƙona masa turare.”


Sai firistoci da Lawiyawa suka tashi suka sa wa jama'a albarka, aka kuwa ji muryarsu, addu'arsu kuma ta kai wurin zamansa a Sama.


Ku zo mu yabi Ubangiji, Dukanku bayinsa, Dukanku waɗanda kuke yi masa hidima, A cikin Haikalinsa da dare.


Ku ɗaga hannuwanku sama, ku yi addu'a a Haikali, Ku yabi Ubangiji!


Ku da kuke tsaye a Haikalin Ubangiji, A wuri mai tsarki na Allahnmu.


“Domin haka ga abin da ni, Ubangiji na ce, Idan ka komo sa'an nan zan kawo ka. Za ka tsaya a gabana. Idan ka hurta abin da yake gaskiya ba na ƙarya ba, Za ka zama kakakina. Za su komo gare ka, Amma kai ba za ka koma wurinsu ba.


Za su zama masu hidima a cikin wurina mai tsarki, suna lura da ƙofofin Haikali, suna hidima a cikin Haikalin. Za su yanka hadayar ƙonawa da ta sadaka domin mutane. Za su lura da mutanen, su yi musu hidima.


“Amma Lawiyawan da suke firistoci daga zuriyar Zadok, waɗanda suka lura da Wuri Mai Tsarki sa'ad da mutanen Isra'ila suka karkace, suka bar bina, su ne za su zo kusa da ni, su yi mini hidima, za su kusace ni domin su miƙa hadaya ta kitse da jini, ni Ubangiji Allah na faɗa.


Sai ya naɗa masa rawani, daga gaban rawanin ya sa allon zinariya, wato, kambi tsattsarka, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.


Sai Haruna ya ta da hannuwansa wajen jama'a, ya sa musu albarka sa'an nan ya sauka daga wurin yin hadaya don zunubi, da hadaya ta ƙonawa, da hadayun salama.


Aikinsu shi ne lura da akwatin alkawari, da tebur, da alkuki, da bagadai, da kayayyakin Wuri Mai Tsarki waɗanda firistoci suke aiki da su, da labule, da dukan aikin da ya shafi waɗannan abubuwa.


“Kawo kabilar Lawiyawa kusa, ka sa su su yi aiki tare da Haruna, firist.


Sa'ad da Haruna da 'ya'yansa maza suka gama kintsa Wuri Mai Tsarki da kayayyakinsa duka a lokacin tashi, sai 'ya'yan Kohat, maza, su zo su ɗauke kayayyakin, amma kada su taɓa abubuwan nan masu tsarki domin kada su mutu. Waɗannan su ne ayyukan 'ya'yan Kohat a duk lokacin da za a naɗe alfarwa ta sujada.


Ba ku kuka zaɓe ni ba, ni ne na zaɓe ku, na sa ku ku je ku yi 'ya'ya, 'ya'yanku kuma su tabbata, domin kome kuka roƙi Uba da sunana yă ba ku.


Sa'ad da suke yi wa Ubangiji ibada, suna kuma yin azumi, Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Sai ku keɓe mini Barnaba da Shawulu domin aikin da na kira su a kai.”


Daga Bulus, bawan Yesu Almasihu, manzo kirayayye, keɓaɓɓe domin yin bisharar Allah,


in ta hidima ce, wajen hidimarmu, mai koyar da Maganar Allah kuwa, wajen koyarwarsa,


Saboda haka, sai ku fito daga cikinsu, Ku keɓe, in ji Ubangiji, Kada ku ko taɓa wani abu marar tsarki, Ni kuwa in yi na'am da ku,


Amma sa'ad da shi wannan da ya keɓe ni tun kafin a haife ni, ya kuma kira ni bisa ga alherinsa, ya ji daɗin


Duk wanda ya yi izgili, ya ƙi yin biyayya da firist wanda yake a can, yana yi wa Ubangiji Allahnku hidima, ko kuma ya ƙi yi wa alƙalin biyayya, to, lalle sai a kashe wannan mutum. Ta haka za ku kawar da mugunta daga cikin Isra'ilawa.


Gama Ubangiji Allahnku ya zaɓe su, su da 'ya'yansu, daga dukan kabilanku don su yi aiki da sunan Ubangiji har abada.


Dattawan garin da ya fi kusa da gawar za su ɗauki karsana wadda ba a taɓa aiki da ita ba, ba a kuma taɓa sa mata karkiya ba.


Sa'an nan sai firistoci, 'ya'yan Lawiyawa, su fito gaba, gama su ne Ubangiji Allahnku ya zaɓa don su yi masa aiki, su sa albarka da sunansa, su ne kuma masu daidaita kowace gardama da cin mutunci.


Sai Musa ya rubuta waɗannan dokoki, ya ba firistoci, 'ya'yan Lawiyawa, waɗanda suke ɗaukar akwatin alkawari na Ubangiji, da dukan dattawan Isra'ila.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan