Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 10:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Ubangiji kuwa ya sāke rubuta dokoki goma a allunan kamar na farko, wato dokoki goma ɗin nan da Ubangiji ya faɗa muku a dutse ta tsakiyar wuta a ranar taron. Sai Ubangiji ya ba ni su.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Ubangiji kuwa ya sāke yin rubutu a waɗannan alluna abin da ya rubuta a allunan farko, wato, Dokoki Goma da ya furta a kan dutse a tsakiyar wuta, a ranar da mutane suka taru. Sai Ubangiji ya ba ni su.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 10:4
10 Iomraidhean Croise  

Sa'ad da ya gama magana da Musa a kan Dutsen Sina'i, sai ya ba shi alluna biyu na shaida, allunan duwatsu rubatattu da yatsan Allah.


Ubangiji ya ce wa Musa, “Sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na farkon, ni kuwa in rubuta kalmomin da suke cikin alluna na farko da ka farfasa.


Musa kuwa yana tare da Ubangiji yini arba'in da dare arba'in, bai ci ba, bai sha ba. Sai ya rubuta kalmomin alkawarin a kan allunan, wato dokokin nan goma.


“Wannan shi ne abin da kuka roƙa a wurin Ubangiji Allahnku a Horeb, a ranar taron, gama kun ce, ‘Kada ka bar mu mu ƙara jin muryar Ubangiji Allahnmu, ko mu ƙara ganin wannan babbar wuta, don kada mu mutu,’


Ubangiji kuwa ya ba ni allunan nan biyu na dutse da shi kansa ya rubuta. A kansu aka rubuta maganar da Ubangiji ya yi muku daga bisa dutsen a tsakiyar wuta a ranar taron.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan