Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 10:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Ni kuma zan rubuta a allunan maganar da take kan alluna na farko waɗanda ka farfashe. Za ka ajiye su cikin akwatin.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Ni kuwa zan yi rubutu a kan allunan nan biyu, kalmomin da suke a alluna na farko, waɗanda ka farfashe. Za a ajiye su a cikin akwatin.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 10:2
9 Iomraidhean Croise  

Ba kome a cikin akwatin alkawarin, sai dai alluna na dutse guda biyu waɗanda Musa ya ajiye a ciki tun a Horeb, inda Ubangiji ya yi alkawari da jama'ar Isra'ila sa'ad da suka fito daga ƙasar Masar.


Ba kome cikin akwatin sai alluna biyu waɗanda Musa ya sa a ciki sa'ad da suke a Horeb. A Horeb ne Ubangiji ya ƙulla alkawarin da mutanen Isra'ila, sa'ad da suka fito daga Masar.


Yana kusato zango, sai ya ga siffar ɗan maraƙi, mutane na ta rawa. Musa kuwa ya harzuƙa, ya watsar da allunan da suke hannunsa a gindin dutsen, suka farfashe.


Ubangiji ya ce wa Musa, “Sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na farkon, ni kuwa in rubuta kalmomin da suke cikin alluna na farko da ka farfasa.


Sai ya ɗauki dokoki goma ɗin, ya sa a akwatin, ya kuma zura sandunan a ƙawanen akwatin, sa'an nan ya sa murfin a bisansa.


Na sauko daga dutsen, na ajiye allunan cikin akwatin da na yi, a nan suke kamar yadda Ubangiji ya umarce ni.”


Shi ne ya hurta muku shari'ar da ya umarce ku ku kiyaye, wato dokokin nan goma. Ya rubuta su a allunan dutse guda biyu.


A cikinsa kuwa da faranti na zinariya domin ƙona turare, da kuma akwatin alkawari da aka yi masa laffa da zinariya ta kowane gefe. A cikinsa kuwa akwai tasar zinariya da manna a ciki, da sandar Haruna wadda ta yi toho, da kuma allunan dutse na alkawarin nan.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan