Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 1:7 - Littafi Mai Tsarki

7 Ku tashi, ku yi gaba zuwa ƙasar duwatsun Amoriyawa, da dukan maƙwabtansu waɗanda suke a Araba. Ku shiga tuddai, da kwaruruka, da Negeb, da bakin bahar, da ƙasar Kan'aniyawa, da Lebanon, har zuwa babban kogi, wato Kogin Yufiretis.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Ku tashi, ku ci gaba zuwa ƙasar tudun Amoriyawa; ku tafi wurin dukan maƙwabta a cikin Araba, a cikin duwatsu, a gindin yammancin tuddai, a Negeb da kuma a ta kwaruruka, da ƙasar Kan’aniyawa da kuma zuwa Lebanon, har zuwa babban kogi, wato, Yuferites.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 1:7
19 Iomraidhean Croise  

Abram kuwa ya ci gaba da tafiya, ya nufi zuwa wajen Negeb.


Dawuda kuma ya ci Hadadezer ɗan Rehob, Sarkin Zoba, da yaƙi lokacin da shi Hadadezer yake kan tafiya zuwa Kogin Yufiretis don ya tabbatar da ikonsa a wurin.


Dawuda kuma ya ci Hadadezer, Sarkin Zoba, da yaƙi a Hamat, sa'ad da ya tafi ya kafa mulkinsa a Kogin Yufiretis.


Ya kuma zauna wajen gabas, har zuwa goshin jejin da yake wajen Kogin Yufiretis, saboda shanunsu sun ƙaru a ƙasar Gileyad.


Zan yanka muku kan iyaka daga Bahar Maliya zuwa tekun Filistiyawa, daga jeji kuma zuwa Kogin Yufiretis. Gama zan ba da mazaunan ƙasar a hannunku, za ku kore su daga gabanku.


“Amma ga shi, saboda ku na hallakar da Amoriyawa, Dogayen mutanen nan masu kama da itatuwan al'ul, Ƙarfafa kuma kamar itatuwan oak, Na hallaka su ƙaƙaf.


Isra'ilawa kuwa suka tashi daki-daki daga jejin Sinai. Girgijen kuma ya tsaya a jejin Faran.


“Sai muka tashi daga Horeb, muka ratsa babban jejin nan mai bantsoro wanda kuka gani a hanyarmu zuwa ƙasar tuddai ta Amoriyawa, kamar yadda Ubangiji Allahnmu ya umarce mu, muka zo Kadesh-barneya.


Amma ƙasar da za ku haye ku mallaka, ƙasa ce ta tuddai da kwaruruka wadda ruwan sama yake shayar da ita.


Duk inda tafin ƙafarku ya taka kuma zai zama naku. Iyakarku za ta kama daga jeji zuwa Lebanon da kuma daga Kogin Yufiretis zuwa Bahar Rum.


Tun daga jejin, da Lebanon, har zuwa babban kogin, wato Kogin Yufiretis, da dukan ƙasar Hittiyawa zuwa Bahar Rum wajen yamma, za ta zama ƙasarku.


Haka nan kuwa Joshuwa ya cinye dukan ƙasar tuddai, da Negeb, da filayen kwaruruka, da gangare, da sarakunansu duka, ba wanda ya ragu, amma ya hallaka su duka kamar yadda Ubangiji, Allah na Isra'ila ya umarta.


Idan ba ku da nufi ku bauta wa Ubangiji, to, yau sai ku zaɓi wanda za ku bauta wa, ko gumakan da kakanninku suka bauta wa a wajajen hayin Kogin Yufiretis, ko kuma gumakan Amoriyawa waɗanda kuke zaune a ƙasarsu, amma ni da gidana, Ubangiji za mu bauta wa.”


Sa'ad da dukan sarakunan da suke hayin Urdun, na cikin ƙasar tuddai, da na ƙasar kwari a gefen Bahar Rum har zuwa Lebanon, wato sarakunan Hittiyawa, da na Amoriyawa, da na Kan'aniyawa, da na Ferizziyawa, da na Hiwiyawa, da na Yebusiyawa, suka ji wannan labari,


tana ce wa mala'ikan nan na shida mai ƙaho, “Ka saki mala'iku huɗun nan da suke a ɗaure a gabar babban kogin nan Yufiretis.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan