Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 1:21 - Littafi Mai Tsarki

21 Ga ƙasar a gabanku wadda Ubangiji Allahnku yake ba ku, sai ku haura ku mallake ta yadda Ubangiji Allah na kakanninku ya faɗa muku. Kada ku ji tsoro ko ku firgita.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

21 Duba, Ubangiji Allahnku ya ba ku ƙasar. Ku haura ku mallake ta yadda Ubangiji Allahn kakanninku ya faɗa muku. Kada ku ji tsoro, kada ku fid da zuciya.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 1:21
20 Iomraidhean Croise  

Ka ba su abinci daga sama sa'ad da suka ji yunwa, Ruwa kuma daga dutse sa'ad da suka ji ƙishi, Ka faɗa musu su shiga su mallaki ƙasar da ka yi alkawari za ka ba su.


Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu, Kullum a shirye yake yă yi taimako a lokacin wahala.


Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu, Allah na Yakubu shi ne mafakarmu!


Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu, Allah na Yakubu shi ne mafakarmu!


Kada ka ji tsoro, ina tare da kai, Ni ne Allahnka, kada ka bar kome ya firgita ka. Zan sa ka yi ƙarfi, in kuma taimake ka, Zan kiyaye ka, in cece ka.


Amma Kalibu ya sa mutane su yi shiru a gaban Musa, ya ce, “Bari mu tafi nan da nan mu mallaki ƙasar, gama za mu iya cinta.”


“Ya ku ɗan ƙaramin garke, kada ku ji tsoro, domin Ubanku na jin daɗin ba ku rabo a cikin Mulkin.


Sa'an nan na faɗa muku cewa, ‘Kun iso ƙasar tuddai ta Amoriyawa wadda Ubangiji Allahnmu yake ba mu.


“Sa'ad da kuka tafi yaƙi da magabtanku, idan kun ga dawakai, da karusai, da sojoji da yawa fiye da naku, kada ku ji tsoronsu. Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar yana tare da ku.


ya ce musu, ‘Ku ji, ya ku Isra'ilawa, yau kuna gab da kama yaƙi da magabtanku, kada ku karai, ko ku ji tsoro, ko ku yi rawar jiki, ko ku firgita saboda su.


Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali, kada ku ji tsoro, ko ku firgita saboda su, gama Ubangiji Allahnku yana tare da ku. Ba zai kunyatar da ku ba, ba kuwa zai yashe ku ba.”


Kada ku ji tsoronsu. Ku tuna yadda Ubangiji Allahnku ya yi da Fir'auna da dukan Masarawa.


Kada ku ji tsoronsu, gama Ubangiji Allahnku yana tare da ku, shi Allah ne mai girma, mai banrazana.


Sa'ad da Ubangiji ya aike ku daga Kadesh-barneya, ya ce, ‘Ku hau ku mallaki ƙasar da nake ba ku,’ sai kuka tayar wa umarnin Ubangiji Allahnku, ba ku gaskata shi ba, ba ku kuwa yi biyayya da muryarsa ba.


Saboda haka, ma iya fitowa gabagaɗi, mu ce, “Ubangiji shi ne mataimakina, Ba zan ji tsoro ba. Me mutum zai iya yi mini?”


Ka dāge, ka yi ƙarfin hali, gama kai ne za ka yi jagorar wannan jama'a su mallaki ƙasa wadda na rantse zan ba kakanninsu.


Ashe, ban umarce ka ba? Ka dāge ka yi ƙarfin hali, kada ka firgita ko ka tsorata, gama Ubangiji Allahnka yana tare da kai duk inda za ka.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan