Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 1:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Tafiyar kwana goma sha ɗaya ne daga Horeb zuwa Kadesh-barneya, ta hanyar Dutsen Seyir.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 (Yakan ɗauki kwana goma sha ɗaya daga Horeb zuwa Kadesh Barneya ta hanyar Dutsen Seyir.)

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 1:2
15 Iomraidhean Croise  

Yakubu kuwa ya aiki jakadu a gabansa zuwa wurin Isuwa ɗan'uwansa a cikin ƙasar Seyir a karkarar Edom,


Zan tsaya a dutsen Horeb can a gabanka. Za ka bugi dutsen, ruwa kuwa zai fito domin jama'a su sha.” Musa kuma ya yi haka nan a gaban dattawan Isra'ila.


Wata rana, sa'ad da Musa yake kiwon garken surukinsa, Yetro, firist na Madayana, sai ya kai garken yammacin jeji, har ya zo Horeb, wato dutsen Allah.


Idan za a yi hadaya ta gari daga cikin nunan fari ga Ubangiji, sai a miƙa hadaya ta nunan fari da ɗanyen hatsi wanda aka gasa aka ɓarza.


Musa da Haruna suka shiga alfarwa ta sujada. Da suka fita, sai suka sa wa jama'a albarka. Ɗaukakar Ubangiji kuwa ta bayyana ga jama'a duka.


Suka zo wurin Musa, da Haruna, da dukan taron jama'ar Isra'ila a jejin Faran a Kadesh. Suka faɗa musu labarin tafiyarsu, suka kuma nuna musu amfanin ƙasar da suka kawo.


Haka iyayenku suka yi sa'ad da na aike su daga Kadesh-barneya don su dubo ƙasar.


“Sai muka tashi daga Horeb, muka ratsa babban jejin nan mai bantsoro wanda kuka gani a hanyarmu zuwa ƙasar tuddai ta Amoriyawa, kamar yadda Ubangiji Allahnmu ya umarce mu, muka zo Kadesh-barneya.


Sai Amoriyawa waɗanda suke zaune a ƙasar tuddai suka fito da yawa kamar ƙudan zuma, suka taru a kanku suka bi ku, suka fatattaka ku a Seyir, har zuwa Horma.


“Muka koma cikin jeji ta hanyar Bahar Maliya kamar yadda Ubangiji ya faɗa mini. Muka daɗe muna ta gewaya ƙasar tuddai ta Seyir.


Ka umarci jama'a, su bi yankin ƙasar zuriyar Isuwa, danginku, waɗanda suke zaune a Seyir. Za su ji tsoronku, sai ku yi hankali,


“Muka yi gaba, muka bar zuriyar Isuwa 'yan'uwan nan namu waɗanda suke zaune a ƙasar tuddai ta Seyir, muka bar hanyar Araba, da hanyar Elat da Eziyon-geber. Muka juya, muka nufi wajen jejin Mowab.


Sa'ad da Ubangiji ya aike ku daga Kadesh-barneya, ya ce, ‘Ku hau ku mallaki ƙasar da nake ba ku,’ sai kuka tayar wa umarnin Ubangiji Allahnku, ba ku gaskata shi ba, ba ku kuwa yi biyayya da muryarsa ba.


Mutanen Yahuza suka je wurin Joshuwa a Gilgal, sa'an nan Kalibu, ɗan Yefunne Bakenizze, ya ce masa, “Ka dai san maganar da Ubangiji ya yi wa Musa, mutumin Allah, a Kadesh-barneya a kaina.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan