Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 1:16 - Littafi Mai Tsarki

16 “A wannan lokaci kuma na umarci shugabanninku na ce, ‘Ku yi adalci cikin shari'a tsakanin 'yan'uwanku, tsakanin mutum da ɗan'uwansa, ko kuma da baren da yake zaune tare da shi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Na kuma umarci alƙalanku a wancan lokaci, na ce, “Ku yi adalci cikin shari’a tsakanin ’yan’uwanku, ko damuwar tana tsakanin ’yan’uwa Isra’ilawa ne, ko kuwa tsakanin Isra’ilawa da baƙin da suke zaune a cikinku.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 1:16
22 Iomraidhean Croise  

Wannan ya yi nesa da kai, da ka aikata irin haka, wato da za ka aza mai adalci daidai yake da mugu! Wannan ya yi nesa da kai! Mahukuncin dukan duniya ba zai yi adalci ba?”


Allah na Isra'ila ya yi magana, Matsaron Isra'ila ya ce mini, ‘Sarkin da yake mulkin mutane da adalci, Wanda yake mulki da tsoron Allah,


Hakika za ku yanka daidai, ku manya? Za ku shara'anta wa mutane daidai?


“Kada ku wulakanta baƙo ko ku zalunce shi, gama dā ku baƙi ne a ƙasar Masar.


Ka yi magana dominsu, ka yi shari'ar adalci, ka kiyaye hakkin matalauta da masu bukata.”


“Ku yi gaskiya da adalci cikin shari'a, kada ku ma ku yi wa matalauci son zuciya, ko ku goyi bayan mawadaci.


Irin shari'ar da za a yi wa baƙo, ita za a yi wa ɗan gari, gama ni ne Ubangiji Allahnku.”


ka sa shi ya tsaya a gaban Ele'azara, firist, da gaban dukan taron, sa'an nan ka keɓe shi a gabansu.


Kada ku yi hukunci da zato, amma ku yi hukunci da adalci.”


Don haka na ɗauko shugabannin kabilanku masu hikima, waɗanda suka saba da ma'amala da jama'a, na sa su shugabanni a gabanku, waɗansu suka zama shugabanni a kan dubu dubu, waɗansu a kan ɗari ɗari, waɗansu a kan hamsin hamsin, waɗansu kuma a kan goma goma. Na sa su zama shugabanni a kabilanku.


“Kada ku zalunci ɗan ƙodago wanda yake matalauci, ko shi danginku ne, ko kuwa baƙon da yake zaune a garuruwan ƙasarku.


“Idan wata gardama ta tashi tsakanin mutane, suka je gaban shari'a, alƙalai kuwa suka yanke musu maganar, suka kuɓutar da marar laifi, suka kā da mai laifin,


A wannan rana kuma Musa ya umarci jama'a, ya ce,


Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Lokacin rasuwarka ya yi, sai ka kira Joshuwa, ku shigo alfarwa ta sujada, don in ba shi ragamar mulki.” Sai Musa da Joshuwa suka tafi, suka shiga alfarwa ta sujada.


Domin kun san yadda muka yi wa kowannenku gargaɗi kamar uba da 'ya'yansa ne, muna ta'azantar da ku, muna kuma ƙarfafa muku umarnin, cewa


Na gama ka da Allah, da Almasihu Yesu, da kuma zaɓaɓɓun mala'iku, ka kiyaye waɗannan abubuwa ƙwarai da gaske, kada ka yi kome da tāra.


Masu dukiyar duniyar nan kuwa ka gargaɗe su kada su nuna alfarma, kada kuwa su dogara da dukiya marar tabbata, sai dai ga Allah, wanda yake ba mu kome a yalwace don mu ji daɗinsa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan