Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 1:11 - Littafi Mai Tsarki

11 Ubangiji Allah na kakanninku ya riɓa yawanku har sau dubu, ya sa muku albarka yadda ya alkawarta muku!

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 Bari Ubangiji, Allahn kakanninku yă ƙara yawanku sau dubu, yă kuma albarkace ku yadda ya yi alkawari!

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 1:11
16 Iomraidhean Croise  

Sai Ubangiji ya fito da shi waje ya ce, “Ina so ka dubi sararin sama, ka kuma ƙidaya taurari, in kana iya ƙidaya su.” Sai kuma ya ce masa, “Haka zuriyarka za ta zama.”


hakika zan sa maka albarka, zan riɓaɓɓanya zuriyarka kamar taurarin sama, kamar yashi kuma a gāɓar teku. Zuriyarka za su mallaki ƙofar maƙiyanka,


Zan riɓaɓɓanya zuriyarka kamar taurarin sararin sama, zan kuwa ba zuriyarka dukan waɗannan ƙasashe, ta wurin zuriyarka kuma al'umman duniya duka za su sami albarka,


Ta wurin Allah na mahaifinka wanda zai taimake ka, Ta wurin Allah Mai Iko Dukka wanda zai sa maka albarka Albarkun ruwan sama daga bisa, Da na zurfafa daga ƙarƙashin ƙasa, Da albarkun mama da na mahaifa.


Amma Yowab ya ce wa sarki, “Ubangiji Allahnka ya sa mutanenka su ƙaru har sau ɗari fiye da yadda suke, har ubangijina sarki ya gani da idonsa, amma me ya sa sarki yake so ya yi wannan abu?”


Amma Yowab ya ce, “Ubangiji ya riɓaɓɓanya yawan jama'arsa har sau ɗari bisa kan yadda suke a yanzu! Ranka ya daɗe, ya sarki, ashe, dukkansu ba naka ba ne? Me zai sa shugabana ya so a yi haka? Me zai sa ya zama sanadin tuntuɓe ga mutanen Isra'ila?”


Ubangiji ya ba ku 'ya'ya, Ku da zuriyarku.


Ka tuna da bayinka Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, waɗanda kai da kanka ka rantse musu, ka ce, ‘Zan riɓaɓɓanya zuriyarku kamar taurarin sama, in kuma ba ku wannan ƙasa duka da na alkawarta zan bayar ga zuriyarku. Za su kuwa gāje ta har abada’ ”


Na sa kin girma kamar tsiro a cikin saura. Kika yi girma, kika yi tsayi, kika zama cikakkiyar budurwa, kika yi mama, gashin kanki kuwa ya yi tsawo, amma duk da haka tsirara kike tik a lokacin.


Allah kuwa ya ce wa Bal'amu, “Ba za ka tafi tare da su ba, ba kuwa za ka la'anta su ba, gama albarkatattu ne su.”


Idan suka sa wa jama'a wannan albarka sa'ad da suke addu'a ga Ubangiji domin Isra'ilawa, Ubangiji zai sa musu albarka.


gama Ubangiji ya riɓaɓɓanya ku, har yawanku ya kai kamar taurarin sama.


Ƙaƙa ni kaɗai zan iya ɗaukar nawayarku da wahalarku da kuma faɗace-faɗacenku?


Duba, na sa ƙasar a gabanku, sai ku shiga ku mallake ta, ƙasa wadda na rantse wa kakanninku, wato Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, cewa zan ba su, su da zuriyarsu a bayansu.’ ”


Kakanninku saba'in ne suka gangara zuwa Masar, amma yanzu Ubangiji Allahnku ya riɓaɓɓanya ku, kuka yi yawa kamar taurarin sama.”


Ko da yake kuna da yawa kamar taurarin sama, za ku zama 'yan kaɗan, domin ba ku yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku ba.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan