Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mika 7:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Sun himmantu su aikata abin da yake mugu da hannuwansu. Sarki da alƙali suna nema a ba su hanci, Babban mutum kuma yana faɗar son zuciyarsa, Da haka sukan karkatar da zance.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Dukan hannuwansu sun gwaninta wajen yin mugunta; shugabanni suna nema a ba su kyautai, alƙalai suna nema a ba su cin hanci, masu iko suna faɗar son zuciyarsu, duk suna ƙulla makirci tare.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mika 7:3
26 Iomraidhean Croise  

Ka kula da mutane masu murguɗa baki suna kaɗa gira a kanka, sun yi tunanin wani mugun abu ke nan.


Alƙalai marasa gaskiya suna cin hanci a ɓoye, sa'an nan ba za su aikata adalci ba.


Shugabanninku 'yan tawaye ne, abokan ɓarayi, a koyaushe sai karɓar kyautai suke yi, da rashawa. Amma ba su taɓa kare marayu a ɗakin shari'a, ko su kasa kunne ga ƙarar da gwauraye suka kawo ba, wato matan da mazansu suka mutu.


Ubangiji yana zuwa ya hukunta jama'arsa a duniya saboda zunubansu. Kashe-kashen da aka yi a duniya a ɓoye, za a bayyana su, ƙasa ba za ta ƙara ɓoye waɗanda aka kashe ba.


Za a yi ta cutar juna. Matasa ba za su girmama manyansu ba, talakawa ba za su girmama na gaba da su ba.


Mugu ne shi, yana kuwa yin mugayen abubuwa, yakan yi shiri don ya lalatar da matalauta da ƙarya, ya kuma hana su samun hakkinsu.


Amma kukan ƙyale masu laifi waɗanda suka ba ku rashawa, kukan kuwa ƙi yi wa marasa laifi shari'ar gaskiya.


Za ka dinga yin fushi da ni? Za ka husata da ni har abada?’ Ga shi, ke kika faɗa, amma ga shi, kin aikata dukan muguntar da kika iya yi.”


Ubangiji ya ce, “Mutanena wawaye ne, Ba su san ni ba, Yara ne dakikai, Ba su da ganewa. Suna gwanance da aikin mugunta, Amma ba su san yadda za su yi nagarta ba.”


Saboda haka zan ba da matansu ga waɗansu, Gonakinsu kuma ga waɗanda suke cinsu da yaƙi, Saboda tun daga ƙarami har zuwa babba Kowannensu yana haɗamar cin muguwar riba, Tun daga annabawa zuwa firistoci Kowannensu aikata ha'inci yake yi.


A cikinka mutane suka karɓi toshi don su zub da jini. Kana ba da rance da ruwa da ƙari, kana kuma cin riba a kan maƙwabcinka saboda cutar da kake yi masa, ka kuwa manta da ni, ni Ubangiji na faɗa.


Shugabanninta sun zama kamar kyarketai masu yayyage ganima. Suna yin kisankai don su sami ƙazamar riba.


Ga shi, kowane shugaban Isra'ila da yake cikinka ya himmantu ga zub da jini bisa ga ikonsa.


Domin kun tunkuɗe marasa ƙarfi da kafaɗunku, kun kuma tunkuye su da ƙahoninku, har kun watsar da su.


Sa'an nan ya ce mini, “Zunubin mutanen Isra'ila da Yahuza ya kasaita ƙwarai. Ƙasar tana cike da jini, birnin kuma yana cike da rashin imani, gama sun ce, ‘Ubangiji ya rabu da ƙasar, ba ya ganinmu.’


Su taron mashaya ne kawai, Karuwai ne kuma. Suna ƙaunar abin kunya.


“Suna faranta zuciyar sarki da muguntarsu, Na shugabanni kuma da ƙarairayinsu.


Na san irin zunuban da kuke yi, Da mugayen laifofin da kuka aikata. Kuna wulakanta mutanen kirki, Kuna cin hanci, Kuna hana a yi wa talakawa shari'ar adalci a majalisa.


Ubangiji ya amsa ya ce, “Ba da daɗewa ba mutanena sun tashi kamar maƙiyi, Kukan tuɓe rigar masu wucewa da salama, masu komawa da yaƙi.


Shari'ar shugabannin ƙasar ta cin hanci ce. Firistocinta suna koyarwa don neman riba, Haka kuma annabawa suna annabci don neman kuɗi. Duk da haka suna dogara ga Ubangiji, suna cewa, “Ai, Ubangiji yana tsakiyarmu, Ba masifar da za ta same mu.”


Amma kuna ƙin nagarta, kuna ƙaunar mugunta, Kuna feɗe mutanena, Kuna kuma fizge naman jikinsu daga ƙasusuwansu.


ya ce, “Me za ku ba ni, in na bashe shi a gare ku?” Sai suka ƙirga kuɗi azurfa talatin, suka ba shi.


Don haka, kada ku yanke wani hukunci tun lokaci bai yi ba, kafin komowar Ubangiji, wanda zai tone al'amuran da suke ɓoye a duhu, ya kuma bayyana nufin zukata. A sa'an nan ne, Allah zai yaɓa wa kowa daidai gwargwado.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan